Jam’iyyar adawa ta ADC ta ce ta lura da wani abu da ta kira “yunƙurin maƙiya na matsa wa shugaban Hukumar Zaɓe ta Kasa (INEC), Farfesa Joash Ojo Amupitan (SAN) lamba”, da nufin dagula shugabancin jam’iyyar a karkashin jagorancin Sanata David Mark.
Wata sanarwa da kakakin jam’iyyar Malam Bolaji Abdullahi ya fitar aka kuma wallafa a shafinta na X, ta ce sun lura cewar tun daga lokacin da ADC ta rabauta da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, fargaba da tsoro suka baibaiye APC.
Sanarwar ta ƙara da cewa wasu manyan jami’an Gwamnatin Tarayya sun sabunta hare-harensu a kan jam’iyyar ADC, da nufin tsoratar da wasu manyan mutane da ke son shiga.
Malam Bolaji ya yi zargin cewa an ƙullo makircin karkata hankali kan sabunta wata takaddamar shari’a ta hanyar mayar da ita gaban kotu.
A ranar 28 ga Maris na 2026 ne wata tawagar manyan lauyoyi (SAN) ta bukaci INEC ta aiwatar da wata fassara mai ban mamaki game da wani hukuncin Kotun Daukaka Kara.
Lawyoyin sun nemi sanin matsayin shari’a gabanin buɗewa ko sabunta shari’ar.
A cewar ADC, ana yi wa shugaban INEC barazanar kama shi idan har bai amince da wannan buƙata a cikin kwanaki bakwai ba.
Sannan ana son INEC ta soke Babban Taron ADC na Kasa, kana ta tsige shugabannin da aka sani tare da miƙa ragamar jam’iyyar ga wani mutum guda, duk da cewa kotu ba ta kammala yanke hukunci kan shari’ar ba.
Gwamnatin Tarayya dai ta sha musanta zargin cewa tana yi wa jam’iyyun adawa zagon kasa ko kutungwila.
A baya dai jam’iyyar ADC ta sha fama da rikicin cikin gida dangane da ƙarewar wa’adin shekaru 17 na jagorancin Ralph Nwosu, tare da miƙa riƙon jam’iyyar hannun Sanata Patricia Akwashiki.
Hakan ta kai ga darewar jam’iyyar gida biyu, inda Honarabul Nafiu Bala Gombe ya kasance Babban Sakatare kuma mai magana da yawun jam’iyyar a ɓangaren masu adawa da jagorancin Nwosu.
A shekarar da ta gabata ne dai Sanata David Mark ya zama shugaban jam’iyya na riƙo bayan wani taro na musamman da aka yi a Abuja.
A halin da ake ciki dai, tsohon ɗan takarar shugabancin ADC. Dumebi Kachikwu, ya ƙi amincewa da shugabancin David Mark.
Su ma ɓangaren Nafiu Bala sun garzaya gaban kotu don kalubalantar INEC a kan amicewa da shugabancin David Mark din.
A ƙarshen watan Maris ɗin da ya gabata Kotun Daukaka Kara ta yi watsi da shari’ar bisa hujjar rashin bin ƙa’ida ta kuma umarci ɓangarorin biyu su zauna yadda suke har sai an kammala shari’ar farko.