Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma ɗan takarar Shugaban Ƙasa na jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce shawarar da ya yanke ta ficewa daga NNPP ba abu ne mai sauki ba.

Da yake sanar da yin murabus daga jam’iyyar ta NNPP a yau Lahadi a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Kwankwaso ya ce matakin abu ne mai wahala a gare shi a matsayinsa na jigo kuma babban mamba a jam’iyyar, amma ya ga dacewar yin hakan duba da yadda siyasar ƙasar nan take sauyawa a halin yanzu.

“Ina amfani da wannan dama domin bayyana godiyata a kan karramawa da damar da aka ba ni na zama Jagoran Jam’iyya na Ƙasa kuma ɗan takarar Shugaban Ƙasa a zaɓen 2023.

“Sai dai, duba da yanayin siyasar ƙasar nan wadda ke buƙatar sabon tsarin haɗin gwiwaa yanzu, na ga ya zama dole in nemi wani dandali na siyasa wanda zai ba mu damar kawo sauyi na gari ga ƙasarmu,” inji shi

Haka kuma, ya mika saƙon godiya ga Shugaban Jam’iyya na Ƙasa, Ajuji Ahmed, da mambobin Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa (NWC), da Kwamitin Amintattu (BoT), da mambobin Kwankwasiyya baki ɗaya, a kan goyon bayan da suka ba shi.

Rabiu Musa Kwankwaso
A makon jiya Kwankwaso ya karbi bakuncin dan takarar Shugaban Kasa na LP, Peter Obi

Daga ƙarshe, ya tabbatar da cewa zai ci gaba da haɗa kai da duk masu ruwa da tsaki domin samar da makoma mai kyau ga Nijeriya.

A makon da ya gabata ne dai dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar LP a 2023, Peter Obi, ya ziyarci Kwankwaso a Kano a daidai lokacin da ake shagulgulan Sallah Karama.

An alakanta ziyarar da ci gaba da yunkurin da ‘yan adawa suke yi na hada karfi da karfe don tunkarar jam’iyyar APC a Zaben 2027.

An dai jima ana hasashen hada Peter Obi da Kwankwaso a tikitin takarar Shugaban Kasa a jam’iyyar ADC.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *