‘Yan Majalisar Wakilai bakwai daga Jihar Kano sun sauya sheka daga jam’iyyar NNPP zuwa APC mai mulki.
Wasu jiga-jigan jam iyyar ta APC daga Jihar Kano a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf sun halarci zaman majalisar don shaida sauyin shekar.
Tun da farko sai da Shugaban Majalisar ya yi wa manyan baƙin iso gabanin shigowar su.
A wasiƙun da suka aike wa Shugaban Majalisa Tajuddeen Abbas, wakilan sun bayyana rikicin shugabanci da rashin makoma a matsayin dalilan da suka sanya su sauya sheƙa zuwa jamiyyar APC.
Wakilan sun hada da Honarabul Gali Mustafa Tijjani mai wakiltar kananan hukumomin Gaya da Albasu da Ajingi; da Honarabul Muhammad Bello Shehu mai wakiltar Karamar hukumar Fagge; da Honarabul Idris Dankawu mai wakiltar Karamar hukumar Kumbotso.
Sauran sun haɗa da wakilin Karamar Hukumar Nassarawa, Honarabul Hassan Shehu Husaini; da na ƙananan hukumomin Sumaila da Takai, Honarabul Rabi’u Yusuf; da na Gabasawa da Gezawa, Honarabul Muhammed Ciroma.
Sai kuma Honarabul Garba Ibrahim Muhammad, mai wakiltar Karamar Hukumar Gwale.
Wannan sauyin sheka dai yana zuwa ne kwana guda bayan jagoran jam;iyyar ta NNPP kuma dan takararta a zaben Shugaban Kasa na 2023, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso, ya sauya sheka zuwa jam;iyyar adawa ta ADC.
