Yayin da hankula ke ƙara kwanciya a jihar Filato, Gwamna Caleb Mutfwang ya bayyana matuƙar alhininsa dangane da harin da aka kai unguwar Angwan Rukuba da ke ƙaramar hukumar Jos ta Arewa, inda aka rasa rayukan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook, gwamnan ya sake miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga iyalai da dangin waɗanda abin ya shafa, tare da yi wa waɗanda suka ji rauni fatan samun sauƙi cikin gaggawa.
Mutfwang ya tabbatar wa al’ummar jihar cewa gwamnatinsa ta riga ta ɗauki kwararan matakai domin dawo da doka da oda.
Ya kara da cewa an ƙarfafa matakan tsaro a sassan da abin ya shafa, sannan jami’an tsaro na ci gaba da farautar waɗanda suka aikata wannan danyen aiki domin fuskantar shari’a.
Gwamna Muftwang ya ce akwai ɓuƙatar mazauna jihar su kwantar da hankulansu, su kasance masu sanya idanu, sannan su haɗa kai wajen kare zaman lafiya da dorewar tsaro a jihar.
“Ina roƙon mu duka da mu kasance masu natsuwa da haɗin kai yayin da muke aiki tare, domin tabbatar da zaman lafiya da jituwa a jihar mu mai daraja,” inji Gwamna Mutfwang.
Daga nan ya jaddada cewar gwamnati za ta yi duk mai yiwuwa wajen tallafa wa iyalai da ‘yan uwan waɗanda harin ya shafa.
Yawan samun hare-hare a tsakiya da arewacin Najeriya na cigaba da tsananta musamman a baya bayan nan. Wane mataki kuke ganin ya kamata gwamnati ta ƙara ɗauka domin kawo ƙarshen al’amarin. Ku bayyana ra’ayoyinku a sashen sharhi.