Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu zai gana da Gwamna Caleb Mutfwang a kan matsalar tsaron Jihar Filato

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya gayyaci Gwamna Caleb Mutfwang na Filato don shata hanyar magance matsalar tsaron da ta addabi Jihar.

Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Al’umma, Alhaji Muhammad Idris Malagi, wanda ya bayyana hakan ga manema labarai, ya ce za a yi ganawar ne ko wanne lokaci daga safiyar Laraba.

Ministan ya kuma ce wannan gayyata ta biyo bayan ganawar da Shugaban Kasa ya yi ranar Talata da manyan hafsoshin tsaro a kan kisan gillar na Jos.

“Wadannan matakai suna nuna muhimmancin da Gwamnatin Tarayya ta bai wa lamari, da kudurinta na ganin an aiwatar da duk abin da ya wajaba ba tare da bata lokaci ba”, inji Ministan.

Ya kara da cewa Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da aiki kafada-kafada da ta Jihar Filato don kawo karshen matsalar tsaro.

Alhaji Muhammad ya kuma tabbatar wa ’yan Najeriya cewa jami’an tsaro sun dauki mataki jim kadan bayan kai harin, lamarin da ya dakile yaduwar tashin hankali.

Da maraicen ranar Lahadi ne dai wasu ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba suka yi dirar mikiya a kan al’ummmar da ke Angwan Rukuba a Karamar Jos ta Arewa suka fara a kan mai uwa da wabi.

An ba da rahoton mutuwar mutum akalla 28 da jikkatar wasu da dama.

Bayan hari ne aka ba da labarin cewa wasu jama’ar yankin sun fara tare ababen hawa suna kisan mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *