Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Senegal (FSF), Abdoulaye Fall,Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Senegal (FSF), Abdoulaye Fall, ya lashi takobin sa kafar wando daya da hukuncin CAF

Ranar Asabar tawagar Terenga Lions ta Senegal za ta buga wasan sada zumunta da ta White-and-Red ta Peru a filin wasa na Stade de France da ke Paris, babban birnin Faransa.

Sai dai kuma wannan wasa yana zuwa ne a daidai lokacin da ake takkadama a kan  Senegal din ne Zakarun Afirka ko Morocco?

Masoya kwallon kafa a fadin Afirka da ma duniya  dai sun yi kasake suna jiran wannan amsa wadda bisa ga dukkan alamu Kotun Sasanta Takaddamar Wasanni ta Duniya (CAS) ce za ta amsa.

CAS din za ta yi hakan ne kuwa ta hanyar yanke hukunci a kan shawarar Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka (CAF) ta kwace nasarar Senegal a Gasar Cin Kofin Kwallon Kafar Afirka (AFCON).

Hakan dai ya biyo bayan matakin da Senegal ta sha alwashin dauka ne na garzayawa Kotun don kalubalantar wannan hukunci na CAF ta kuma shigar da korafi rannar Laraba.

Ranar Alhamis Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Senegal (FSF), Abdoulaye Fall, ya lashi takobin sa kafar wando daya da wannan hukunci na CAF, wanda ya kwatanta da “fashi”.

“FSF ba za ta rungume hannu tana kallon wannan ‘fashi da makami’ ba. Za mu kaddamar da ‘jihadi’ ta fuskar shari’a”. inji shi.

Hukuncin CAF

Kasar ta Senegal dai ta dauki hayar laiyoyi na gida da na waje don su kalubalanci wannan hukunci na CAF.

Da yake jawabi ga wani taron manema labarai ranar Alhamis, daya daga cikin lauyoyin na hukumar FSF, Juan de Dios Crespo Perez, ya ce “Ba za ma a kalli wannan shawara a matsayin hukunci na adalaci a harkar wasanni ba – rashin adalcin da rashin tsarin da rashin hangen nesan sun isa”.

Ranar 17 ga watan Maris ne dai Hukumar Koli ta Sauraren Korafe-Korafe ta yanke wannan shawara, tana kafa hujja da cewa ficewar da ’yan wasan Senegal suka yi daga fili a wasan karshe na AFCON 2025 ya yi karan tsaye ga Sashe na 82 da Sashe na 84 na Dokokin CAF.

A cewarta, ficewar daidai take da sarayar da wasan, don haka ta yanke hukunci cewa Morocco ce ta yi nasara da ci 3- 0.

Wannan hukunci dai ya saba da wanda Kwamitin Ladabtarwa na CAF din ya yanke a karshen watan Janairu cewa duk da korafin Morocco, Senegal ne Zakarun Afirka na 2025.

Kasancewar wannan hukunci na Hukumar Koli ta CAF ya dauki watanni bayan lamarin kafin bayyana shi ya haifar da takaddama da tayar da jijiyoyin wuya ba kawai a tsakanin kasashen biyu ba, har ma da sauran kasashe.

Hukuncin CAS

Bisa al’ada, CAS takan dauki watanni kafin ta shirya zama a kan wani korafi, sannan ba ta fitar da sakamako sai bayan wasu makwanni.

Sai dai lauyoyin FSF sun sha alwashin ganin ba a bata lokaci ba wajen yanke hukunci a CAS din.

Serge Vittoz, daya daga cikinsu, ya ce: “irin wannan lamari kan dauki wata tara zuwa 12, amma muna so a hanzarta…”

Shi kuwa lauya Seydou Diagne gargdi ya yi: “In har CAS ta amince da wannan hukuncin [na CAF], to a ofishin lauyoyi za a yanke hukunci a kan wanda zai lashe Gasar Cin Kofin Duniya ta gaba”.

Kotun wasanni ta CAS ka iya yanke dayan hukunce-hukunce uku: ko ta goyi bayan hukuncin CAF cewa Morocco ne Zakarun Afirka, ko ta yi fatali da shi ta dawo wa da Senegal nasararta, ko kuma ta tsaya a tsakiya.

Tasirin Hukuncin CAS

Tasirin hukunci na farko Kotun za ta amince cewa ficewar da ’yan wasan Senegal suka yi daga fili sarayar da wasan ne kamar CAF ta fada.

Wannan za isa a hukumance ficewa daga fili ko da na dan kankanin lokaci ne ya zama babban laifi da zai kai ga sarayar da wasa.

Zai kuma karfafa ikon da Hukumar Kolin CAF take da shi a kan alkalancin wasa.

Idan ta yanke hukunci na biyu, wato ta ce a mayar wa Senegal kambunsu, to za ta tabbatar da wani muhimmin al’amari.

Ma’ana, hakan zai nuna cewa abin da alkalan wasa suka yanke a kan wasa shi ne hukunci na karshe, hukumomin kwallon kaf aba su da hurumin sauya sakamako daga baya.

Amma idan CAS ta hau Katanga, to za ta tabbatar wa Senegal nasara, ta kuma ce hukuncin kwace kambun  ya yi tsauri.

Idan haka ta faru, Senegal za su koma matsayinsu na Zakarun Afirka, amma za su biya tara ko su fuskanci dakatrawa ko rage maki a wasannin da za su buga nan gaba.

A nan sai a bai wa Morocco wata ’yar diyya ko a yaba musu ba tare da an ba su kambun ba.

Sannan hukuncin CAS za iyi gagarumin tasiri a kan CAF ta hanyar karfafa ikonta )idan hukuncin ya dace da abin da ta yanke) ko kuma bankado raunin shugabancin a harkar kwallon kafa a Afirka.

Me Ya Yi Zafi?

Wannan takaddama dai ta samo asali ne ranar 18 ga watan Janairu, ranar da aka buga wasan karshe na AFCON 2025 tsakanin Snegal da Morocco a filin wasa na Moulay da ke birnin Rabat.

Ana cikin wasa alklain wasa ya bai wa Morocco bugun daga-kai-sai-mai-tsaron-gida – lamarin da ’yan wasan Senegal bas u ji dadinsa ba.

Don haka ne mai horar da su, Pape Thiaw ya umarce su da su fice daga filin don nuna rashin amincewarsu.

Ba su koma filin ba sai bayan minti 15, lamarin da ya jawo tsaiko ya kuma fusata ’yan kallo. Bayan komawa wasa Moroccon ma suka barar da fanaretin.

Har aka tashi wasa, ba ci. Amma daga karshe Senegal ce ta yi nasara da ci daya mai ban haushi a karin lokaci.

Korafin Morocco

Morocco ta yi korafi game da ficewar ’yan wasan Senegal tana kafa hujja da cewa Terenga Lions din sun sarayar da wasan kamar Sashe na 82 da na 84 na Dokokin CAF suka tanada duk da sun dawo an ci gaba.

Sannan kuma, a cewar Morocco, ficewar ta kalubalanci ikon Alkalin Wasa, lamarin da ya saba da dokokin CAF wadanda suka ce babu ja a kana bin da jami’an wasa suka hukunta.

A ganin su, idan aka kyale Senegal. To nan gaba ma duk wanda wani hukuncin alkalin wasa bai yi mishi dadi ba zai iya ficewa daga fili.

Sannan suka ce matakin na ’yan wasan Senegal cin fuska ne ga Gasar, don haka bai kamata a saka wa wanda ya aikata hakan da matsayin Zakaran Kwallon Kafar Afirk aba.

Daga karshe Morocco ta bukaci CAF ta kwace kambun daga hannun Snegal, sannan ta ayyana ta  a matsayin wadda ta lashe wasan da ci 3 -0.

A Karshe

Yanzu dai a wajen CAF Morocco ne Zakarun Afirka, ko da yake FSF da layoyinta sun ce har yanzu Sengal ne Zakaru.

Hakan na nufin za a ci gaba da takaddama a kan wane ne Zakaran AFCON 2025 har zuwa lokacin da CAS za ta yanke hukunci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *