Tun da safiyar ranar Juma’a mahalarta Babban Taron APC na Kasa suka fara hallara a birnin Abuja.
Taron, wanda za a kwashe kwana biyu ana yi, zai gudana a Dandalin Eagle Square da ke Gundumar Tsakiyar Abuja.
Ministan Yada Labarai kuma Shugaban Kwamitin Yada Labarai na Kwamitin Shirya Taron, Alhaji Muhammad Idris, ya ce daliget 8,453 ne ake sa ran za su halarci taron.

Ya fadi hakan ne yayin wani Taron Manema Labarai na Duniya da Kwamitin ya shirya a Abuja ranar Alhamis.
“Ana sa ran daliget-daliget daga jihohi 36 da Yankin Birnin Tarayya ne za su taru don tattauna manufofin gwamnati da zaben shugabanni da kuma mika ragama ga sababbin shugabannin jam’iyya a hukumance.
“Taron zai kuma samar da wani dandali na yanke shawara da ma waiwaye da shata alkiblar mataki nag aba na [wannan] tafiya tamu”, inji Ministan.
Matakan Tsaro
Tun ranar Alhamis ne dai Ofishin Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya ya sanar da cewa za a rufe Gine-Ginen Sakatariyar Gwamnatin Tarayya, ya kuma umarci ma’aikata a Rukunai na 1 zuwa na 3 da ma ginin Ma’aikatar Harkokin Waje su yi aiki daga gida.
“Don haka ne ake bukatar dukkan Manyan Sakatarori da Shugabannin Hukumomi su sanar da ma’aikatansu, su kuma tabbatar da an yi aiki da wannan umarni”, inji sanarwar mai dauke da sa-hannun wani Babban Sakatare a Ofishin, Dokta Abdul S. U. Garba .
An kuma tsaurara matakan tsaro a daura da Dandalin na Eagle Square, ciki gar da rufe hanyoyin da suka isa can.
Wannan lamari dai ya haifar da cunkoson ababen hawa a wasu sassan birnin, inda aka ga ma’aikata da dama suna takawa don isa wuraren aikinsu.

Cincirindon Magoya Baya
Titunan Abuja har zuwa wadanda suke da tazarar akalla kilomita daga Eagle Square cike suke da magoya bayan ’yan siyasa wadanda suke ta kade-kade da raye suna rera ko suna saka fayafayan wakokin gwanayensu.
Wasu kuwa kai-kawo suke yi dauke da hotunan ’yan siyasar da suke goya wa baya suna rera wakokin yabo a gare su.

Su ma masu saye da sayarwa ba a bar su a baya ba – yayin da wasu suka kasa hajojinsu wasu kewayawa suke yi suna ta ciniki.
