Matatar mai ta Dangote ta ce akwai kuskure a tunanin da ’yan Najeriya suke yi cewa tana sayen danyen mai a Naira don haka bai kamata ta kara farashin tataccen manta ba.
Shugaban Matatar, David Bird, wanda ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Arise da safiyar yau, ya ce duk da Kamfanin Mai na Najeriya (NNPCL) yana sayar musu da danyen mai a Naira, a kan farashin da ake sayarwa a kasuwannin duniya ake cininkin.
A cewarsa, manufar tsarin na sayar da danyen mai a Naira ita daidaita darajar kudin na Najeriya a kasuwar hadahadar kudade, ta yadda za a iya sayen kayan ba tare da an nemo Dala ba.
Mista Bird ya kuma ce duk da bisa tanadin yarjejeniyar da Matatar Dangote ta kula da Gwamnati za a rika sama mata tanka (manyan jiragen ruwa na dakon mai) 13 zuwa 15 duk wata – wanda zai ba ta damar wadata kasar da man fetur – amma tanka biyar kacal take samu a yanzu.
“Abin da muke gani game da farashin mai shi ne, muna kokari mu daidaita lamura ta yadda za mu ci amfanin kasuwar, saboda babu tallafi a kan abin da muke saya”, inji Mista Bird.
Ya kara da cewa yanzu haka Matatar Dangote tana aiki ka’in da na’in, inda take sarrafa gangar mai 650,000 a kullum, wanda take wadata kasuwar mai ta cikin gida da shi, ta kuma fitar zuwa wasu kasashen.
Tun bayan da Amurka da Isra’ila suka fara kai hari a kan Iran ne dai farashin danyen man fetu rya tashi a kasuwannin duniya.
Hakan ne kuma ya sa farashin tataccen man fetur ya tashi a Najeriya, inda yanzu a wasu gidajen main a Abuja ake sayar da lita daya a kan kudi sama da Naira 1,300.
’Yan Najeriya da dama dai sun kasa fahimtar dalilin Matatar Mai ta Dangote na kara farashi, duk da tana samun danyen mai daga Kamfanin NNPCL.
