Shugaba Donald Trump na Amurka ya ce ya umarci Ma’aikatar Tsaron kasarsa ta dakatar da kai hari a kan cibiyoyin makamashin Iran daga yanzu zuwa kwana biyar.
Shugaban ya fadi haka ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, sa’o’i kadan kafin cikar wa’adin da ya bai wa Iran din ta bude Mashigar Hormuz ko Amurka ta kai mata hari.
Trump ya kuma ce ya dauki wannan mataki ne bayan nasarar “wata tattaunawa mai ma’ana da Amurka da kasar Iran suka yi a kwanaki biyu da suka gabata game da kawo karshen takaddama a tsakaninmu a Gabas ta Tsakiya.
“Saboda yadda wannan tattaunawa ta kasance, wadda kuma za ta ci gaba a wannan makon, na bai wa Ma’aikatar Tsaro umarni ta dakatar da duk wani harin soji a kan tashoshin makamashi na Iran a kwana biyar masu zuwa”.
Idan ba a manta ba, Shugaban Kasar na Amurka ya bai wa Iran sa’o’I 48 ta bude Mashigar Hormuz ko Amurka ta kai hari a kan tashoshin samar da wutar lantarki da sauran cibiyoyin makamashi.
Sai dai Iran ta mayar da martini tana barazanar kai hari a kan tashoshin lantarki da cibiyoyin makamshi da ma wuraren tace Ruwan teku na kasashen Gabas ta Tsakiya.
Wannan ne karo na farko da duniya ta ji labarin cewa Amurka na tattaunawa da Iran.
A baya, Shugaba Trump ya ce zai so ya tattauna da shugabannin Jamhutiyar ta Muslunci amma bai san wanda zai tuntuba ba.
Wasu manazarta dai sun nuna shakku game da gargadin na Amurka, suna cewa Trump ya yi subul da baka ne wajen yin gargadin.
Wasu dai suna fassara wannan sanarwa a matsayin tsagaita wuta ta tsawon kwana biyar a yakin da Amurka ta ce Isra’ila ta ingiza ta ta kaddamar a kan Iran.
