Shugaba Bola Tinubu a ranar Alhamis ya ƙalubalanci gwamnonin jihohi shida na shiyyar Arewa maso-Gabas—wato Adamawa da Bauchi da Borno da Gombe da Taraba, da Yobe—da su ƙara ƙaimi wajen fuskantar ƙalubalen ta’addanci da fashin daji.

Ya bayyana cewa tattalin arziƙin Najeriya ya daidaita kuma kasar ta shiga abin da ya kwatanta da sabon zamani (golden age).

Tinubu ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi baƙuncin tawagar shugabannin siyasa da manyan jami’an gwamnati daga shiyyar Arewa maso Gabas a Fadar Shugaban Ƙasaa da ke Aso Rock, Abuja.

Jami’an da suka yi magana da wakilinmu a baya sun bayyana cewa ziyarar ta kasance ta godiya ce ta hukumance biyo bayan matakin Shugaban Ƙasa na rike Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa na zaben shugaban kasa na shekarar 2027.

Tinubu ya fada wa taron cewa: “Ina ganin ƙalubalen da shugabannin Arewa maso Gabas ke fuskanta saboda ta’addanci da fashin daji. Ina ganin haɗin gwiwarmu. Muna aiki tare. Sai kawai idan muka kasance tare, muka yi tunani tare, kuma muka fuskanci ƙalubalen ta hanyar da ta dace a matsayin ƙasa ɗaya mai haɗin kai ne za mu yi nasara.”

Ya ƙara da cewa:”Sabon Zamani ya iso yanzu. Idan za ku iya daidaita tattalin arziƙi, ‘yan Najeriya ba sa buƙatar abubuwa da yawa: kawai zaman lafiya mai ɗorewa da jin daɗin jama’a. Muna kan turba ta gaskiya kuma ba za mu taɓa waiga wa baya ba. Na yi muku alƙawari, Najeriya za ta tsira. Za mu sami haɗin kan mu a cikin bambancin mu, da kyakkyawar hanyar samun kwanciyar hankali na dimokuraɗiyya da nasara. Na yi muku alkawarin hakan.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *