Majalisar Wakilai ta Najeriya ta amince da saurarar ƙudirin gwamnatin tarayya na kafa ’yan sandan jihohi, a wani mataki da ake ganin zai kawo sauyi a tsarin tsaron cikin gida na Najeriya ta hanyar bai wa jihohi damar samun rundunar ’yan sanda ta kan su.
An amince da ƙudirin ne a zaman majalisar da aka gudanar ranar Alhamis, bayan da majalisar ta janye nata ƙudirin gyaran kundin tsarin mulki kan kafa ’yan sandan jihohi, tare rungumar ƙudirin da gwamnatin tarayya ta gabatar, kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
- Majalisar Wakilai ta yi barazanar ɗaukar matakan doka kan Shugaban Hukumar Kula da Haraji ta Ƙasa {NRS}, Zacc Adedeji game da daukar ma aikata
- Cardoso ya gabatar wa Majalisar Dattawa rahoton halin da tattalin arziki ke ciki
- Dangote ya sake komawa sayar da fetur da Naira
Amincewar Majalisar Wakilan ta biyo bayan amincewar Majalisar Dattawa da nata sigar ƙudirin, lamarin da ya ƙara kusantar da Najeriya ga aiwatar da tsarin ’yan sanda biyu, wato na gwamnatin tarayya da kuma na jihohi.
Ana sa ran sabon tsarin zai taimaka wajen ƙarfafa tsaron cikin gida, inganta aikin tabbatar da doka da oda, da kuma bai wa jihohi damar magance matsalolin tsaro da suka shafe su cikin sauri da inganci.