Majalisar Wakilai ta yi barazanar ɗaukar matakan doka kan Shugaban Hukumar Kula da Haraji ta Ƙasa (NRS), Dakta Zacch Adedeji, saboda abin da ta bayyana a matsayin ƙin mutunta ikon Majalisar da kuma kin amsa gayyatar kwamitanta mai kula da ka’idar daidaito tsakanin jihohi (Federal Character).
Kwamitin, ƙarƙashin jagorancin ɗan majalisa Ahmed Idris Wase, ya kuma umarci Hukumar NRS da ta dakatar da duk wani aikin ɗaukar ma’aikata nan take har sai shugabanninta sun bayyana a gabansa domin bayar da bayani kan yadda ake gudanar da aikin.
A zaman kwamitin da aka gudanar ranar Laraba a Abuja, mambobin sun ce tun ranar 15 ga Yulin 2026 sun gayyaci Dakta Adedeji tare da buƙatar ya gabatar da cikakken jerin ma’aikatan hukumar, amma bai halarci zaman ba duk da cewa an tabbatar da karɓar wasiƙar.
-
Cardoso ya gabatar wa Majalisar Dattawa rahoton halin da tattalin arziki ke ciki
-
Majalisar Dattawa ta buƙaci ƙwararan dokoki kan ma’adinai
Kwamitin ya ce wannan ba shi ne karo na farko ba, domin tun daga shekarar 2023 ya aika wasiƙu da dama zuwa ga shugaban NRS, amma ya zarge shi da kin ba da amsa yadda ya kamata duk da cewa ofishinsa ya karɓi wasiƙun.
Rikicin tsakanin Majalisar da Hukumar NRS ya kuma shafi zargin cewa Hukumar Federal Character Commission (FCC) ta ba NRS izinin gudanar da ɗaukar ma’aikata duk da umarnin da kwamitin ya ce ya ba ta na dakatar da irin waɗannan amincewa.
Shugabar FCC, Hulayat Motunrayo Omidiran, ita ma ba ta halarci zaman ba. Ta sanar da kwamitin cewa tana wata tafiya ta aiki kuma ta kamu da rashin lafiya, sai dai kwamitin ya ce yawan ƙin amsa gayyata daga shugabannin hukumomin gwamnati abin damuwa ne kuma ya saɓa wa ƙa’idar riƙon amana.
Ahmed Idris Wase ya ce ikon sa ido da Majalisar Dokoki ke da shi bisa kundin tsarin mulki wajibi ne ga dukkan hukumomin gwamnati su mutunta shi. Ya jaddada cewa babu wata hukuma ko jami’in gwamnati da ya fi ƙarfin kundin tsarin mulkin ƙasa.
Kwamitin ya yi gargaɗin cewa ci gaba da ƙin amsa gayyatar Majalisar na iya raunana amincewar jama’a da tsarin dimokuraɗiyya, yana mai cewa zai yi amfani da dukkan tanade-tanaden kundin tsarin mulki domin tabbatar da bin umarninsa.
Rahotanni daga Majalisar sun nuna cewa ƙin bayyana da shugaban NRS ya yi na iya alaƙa da zargin karya dokar kafa hukumar wajen naɗin wasu manyan daraktoci da kuma ɗaukar ma’aikata. Haka kuma wata ƙungiya mai zaman kanta ta shigar da ƙara a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja tana ƙalubalantar sahihancin naɗin wasu daga cikin daraktocin hukumar.