Karim Adeyemi, sabon dan wasan gaba na Barcelona

Barcelona ta sanya hannu kan kwantiragin shekaru 5 don sayan ɗan wasan gaba na Borussia Dortmund, Karim Adeyemi.

Adeyemi ɗan shekara 24, zai sake haɗuwa da koci Hansi Flick, wanda shi ne ya ba shi damar buga wasansa na farko a tawagar ƙasar Jamus.

Adeyemi ya shafe shekaru 4 a Dortmund tun bayan barin RB Salzburg.

A kakar da ta wuce ya zura ƙwallaye 10 kuma ya bayar da taimako 8 a wasanni 44 da ya buga.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *