Jurgen Klopp, tsohon kocin Liverpool

Ana sa ran gabatar da Jurgen Klopp a matsayin sabon kocin tawagar ƙasar Jamus a ranar Jumma’a.

Kafar Sky ta ruwaito cew an cimma cikakken yarjejeniya da tsohon kocin na Liverpool don ya jagoranci ƙasarsa ta haihuwa, da kwantiragi da zai kai har zuwa Gasar cin Kofin Duniya ta 2030.

Har ila yau Red Bull sun kammala tsarin sallamar Klopp daga muƙaminsa na shugaban ƙwallon ƙafa na duniya na kamfanin, domin ya samu damar komawa DFB.

Ana sa ran Klopp zai maye gurbin Julian Nagelsmann, bayan da Jamus ta fice daga Gasar cin Kofin Duniya a zagaye na 32 a bugun fenareti a hannun Paraguay.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *