Yayin da hare-haren da Amurka ke kai wa Iran ke ci gaba, mashigar Hormuz da kuma mashigar Bab el-Mandeb sun sake fuskantar matsalar rufe hanya ga zirga-zirgar jiragen ruwa.

Rundunar Sojojin Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran (Revolutionary Guard) ta fitar da wani bidiyo a ranar Laraba da ke nuna, yadda ake harba makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa zuwa sansanonin sojojin Amurka da ke Jordan.

Amurka ta shafe dare 12 a jere tana kai hare-hare kan Iran, inda ta riƙa kai hari kan wurare daban-daban a faɗin ƙasar.

Tehran ta yi gargaɗin cewa za ta mayar da martani mai ƙarfi idan aka kai hari kan muhimman wuraren fararen hula.

Iran ta kuma sanar da cewa ta dakatar da wasu jiragen ruwa uku masu ɗauke da mai da ke ƙoƙarin wucewa ta mashigar Hormuz.

Kafin fara yaƙin a Iran, kusan ganga miliyan 15 na mai a kowace rana ne ake jigilar su ta wannan mashigar daga yankin Tekun Fasha.

Hanyar da ake amfani da ita ta Tekun Bahar Maliya (Red Sea) ma na fuskantar barazana, bayan da a farkon wannan makon akalla jiragen ruwa tara suka juya baya a kusa da mashigar Bab el-Mandeb sakamakon gargadin da ‘yan tawayen Houthi masu samun goyon bayan Iran suka yi.

A ranar Litinin, shugabannin Houthi a Yemen sun sanar da kafa shingen ruwa kan Saudi Arabiya bayan wani hari da aka kai a filin jirgin saman Sana’a a makon da ya gabata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *