Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Mista Olayemi Cardoso, ya gabatar wa Kwamitin Majalisar Dattawa kan bankuna, Inshora da Cibiyoyin Kudi rahoton ayyukan sa, na zangon farko na shekara ta 2026 kamar yadda doka ta tanada a ranar Laraba, 22 ga Yulin 2026.

Yayin gabatar da rahoton, Gwamnan ya zayyano irin ci gaba da yace bankin ya samu ta fuskokin samun sassaucin hauhawar farashi, daidaituwar kasuwar musayar kudaden waje, haɓakar adadin kudaden da ake ajiyewa a ketare, juriya da ƙarfafar ɓangaren bankuna, gami da sauye-sauye a tsarin kasuwanci.

Ya zayyana abubuwan da bankin zai sa a gaba a zango na biyu na shekarar 2026, waɗanda suka haɗar da sa ido a kan bankuna, faɗaɗa sauye-sauyen kasuwar musayar kudaden waje, hauhawar farashi, aiwatar da tsarin biyan Kudi na 2028, tsaron yanar gizo, da kuma kiyaye daidaiton tsarin kuɗi na ƙasa.

Yayin da yake hasashen makomar tattalin arzikin Nijeriya, Cardoso ya ce CBN zai ci gaba da yanke shawarwari bisa la’akari da nauyin da doka ta ɗora masa, bisa la’akari da muradun ‘yan Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *