Babban Bankin Najeriya

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya umarci bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi a faɗin ƙasar nan da su gaggauta daskarar da duk wasu asusu, kadarori da ke da alaƙa da wasu mutane shida da kamfanonin canjin kuɗi (BDC) guda huɗu da aka sanya a jerin masu ɗaukar nauyin ayyukan ta’addanci.

Umarnin na kunshe ne a cikin wata takarda mai lamba CMD/FCS/PUB/CIR/002/011 da aka bankin ya fitar ranar 24 ga Yunin 2026.

A cewar Babban Bankin, sabon Jerin Takunkuman Najeriya (Nigeria Sanctions List), wanda ya fara aiki daga ranar 18 ga Yunin 2026, wajibi ne ga dukkan cibiyoyin kuɗi da ke ƙarƙashin kulawarsa su aiwatar da shi ba tare da wani jinkiri ba.

Wannan mataki ya biyo bayan takunkumin da Ma’aikatar Kuɗi ta Amurka, ta hannun Ofishin Kula da Kadarorin Ƙasashen Waje (OFAC), ta sanya wa wani ɗan Najeriya mai suna Mukhtar Adamu da wasu kamfanonin canjin kuɗi uku bisa zargin taimakawa wajen ɗaukar nauyin ƙungiyar ta’addanci ta ISWAP (Islamic State West Africa Province).

Bayan matakin Amurka, gwamnatin Najeriya ta kuma fitar da jerin sunayen wasu mutane da kamfanoni da aka sanya wa takunkumi kan zargin ɗaukar nauyin ayyukan ta’addanci.

Mutanen da aka sanya a jerin sun haɗa da Ibrahim Yakubu Ogirima, Adamu Chiroma, Ibrahim Abubakar, Abdullahi Umar Usman, Babangida Muhammed da Adamu Hammajam.

Kamfanonin da aka sanya wa takunkumi kuwa sun haɗa da Abbal Bako & Sons Bureau De Change Limited, Generation Currency BDC Limited da Nine to Nine BDC Limited.

Da yake mayar da martani kan batun, Shugaban Ƙungiyar Masu Sana’ar Canjin Kuɗi ta Najeriya (ABCON), Aminu Gwadebe, ya yi gargadin kada a ɗauki laifin wasu tsirarun masu sana’ar BDC a matsayin laifin daukacin masana’antar.

Ya bayyana cewa mafi yawan kamfanonin BDC masu lasisi a Najeriya suna bin dokoki da ƙa’idojin da hukumomi suka gindaya tare da gudanar da ayyukansu bisa tanadin doka.

Gwadebe ya buƙaci masu ruwa da tsaki da jama’a da su bambance tsakanin kamfanonin da aka sanya wa takunkumi da kuma halastattun masu gudanar da sana’ar BDC, yana mai cewa masana’antar na ci gaba da goyon bayan matakan da hukumomi ke ɗauka domin ƙarfafa gaskiya da yaƙi da laifukan kuɗi.

Ya ƙara da cewa masu lasisi za su ci gaba da haɗa kai da hukumomin da abin ya shafa domin kare mutuncin tsarin kuɗi na ƙasa tare da tabbatar da bin dokokin yaƙi da halatta kuɗaɗen haram da kuma hana ɗaukar nauyin ayyukan ta’addanci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *