Tsohon Ministan Sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami, ya karɓi takardar shaida daga Jam’iyyar PDP, wadda ta tabbatar da shi a matsayin ɗan takarar gwamna na jam’iyyar a zaɓen gwamnan Jihar Gombe na 2027.
Pantami, ya karɓi takardar ne ranar Laraba yayin taron rantsar da Kwamitin Zartarwa na Jam’iyyar na Ƙasa na 2026–2030 a shelkwatar PDP ta ƙasa da ke Abuja.
A cewar wata sanarwa da kwamitin yaɗa labarai ta Pantami ta fitar, shugaban Jam’iyyar PDP na Ƙasa, Abdulrahman Mohammed ne ya jagoranci taron.
-
Akpabio ya rantsar da sabbin Sanatoci 4
-
Ƙudirin kafa ƴan sandan jihohi ya samu sabon ci gaba, bayan da Majalisar Dattawa ta amince da shi
Sanarwar ta ce jam’iyyar ta yi amfani da wannan damar wajen miƙa Takardun Shaida ga ’yan takarar gwamna waɗanda Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa ta amince da kuma wallafa sunayensu a matsayin waɗanda PDP ta zaɓa bisa ƙa’ida don babban zaɓen 2027.
Ta ƙara da cewa Pantami na daga cikin ’yan takarar da aka miƙa musu takardun, inda ta bayyana hakan a matsayin tabbatar da matsayinsa a matsayin ɗan takarar gwamna da jam’iyyar ta amince da shi a hukumance a Jihar Gombe.
“PDP ta miƙa Takardun Shaida ga ’yan takararta na gwamna na zaɓen 2027 waɗanda INEC ta amince da kuma wallafa sunayensu a matsayin waɗanda jam’iyyar ta zaɓa bisa ƙa’ida,” in ji sanarwar.