Masu ruwa da tsaki daga fannoni daban-dabam ciki har da jami’an Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Najeriya NFF, sun halarci jana’izar karshe ga tsohon Kocin Najeriya, Cif Osuolale Bolarinwa Adegboye Onigbinde, wanda aka yi a jihar Osun.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da daraktan sadarwa na Hukumar NFF, Ademola Olajire, ya aike wa gidan Rediyon Blueprint dake Abuja, a ranar Asabar.

A cewar sanarwar, marigayin ya samu yabo kan gudumuwar da ya bayar wanda suka hada da shi ne koci dan asalin Najeriya na farko da ya kai tawagar manyan maza ta Najeriya wasan  ƙarshe na Kofin Kasashen nahiyar Afirka, kuma koci dan asalin Najeriya na farko da ya jagoranci Super Eagles a gasar cin Kofin Duniya.

Tsohon kyaftin kuma kocin Najeriya, Augustine Eguavoen, wanda ya yi magana a madadin NFF, ya ce marigayi Cif Onigbinde ya yi tasiri sosai a rayuwarsa ta harkar ƙwallon ƙafa.

“NFF ta yaba wa hidimar da marigayi Cif Onigbinde ya yi wa ƙasarmu.

Mutum ne mai kuzari kuma ya kai kololuwar sana’ar ta hanyar jajircewa da sadaukarwa da ladabi. Ya kasance wani babban abin hange a fannin koyar da ƙwallo a duniya.

“Shi ne dan Najeriya na farko da ya jagoranci Super Eagles din mu zuwa lashe lambobin azurfa a Kofin ƙasashen Afirka, sannan ya zama dan Najeriya na farko da ya jagorance su a gasar cin Kofin Duniya.

Ko da ya yi ritaya, ya ci gaba da ba da gudummawa sosai ta hanyar zama malami a wajen koyar da ilimin kwallo na NFF…muna addu’ar Allah ya jikansa kuma ya ba iyalin da ya bari da masu harkar kwallon kafa ta Najeriya baki ɗaya haluri.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *