Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya ta kama wasu ’yan’uwa biyu, Emmanuel Eugene mai shekara 18 da Kelvin Eugene mai shekara 20, bisa zargin yi wa wata yarinya mai shekara 15 fyade a jihar Delta.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a titin Okoro da ke yankin Third Marine Quarters a Ƙaramar Hukumar Warri ta kudu a Jihar Delta, a watan Yunin 2026.

An ce mahaifiyar yarinyar ta bar ta a gida domin kula da ƙaninta yayin da ta tafi kasuwa, sai dai daga bisani aka rasa inda ta shiga.

Bayan fara neman ta, wani maƙwabci ya shaida wa iyalanta cewa an ga yarinyar a kusa da gidan waɗanda ake zargin a ranar da ta ɓace.

Daga baya wata mata ta gano ta a cikin wata coci da ke Effurun, inda ta sanar da iyalanta.

Rahotanni sun ce da farko yarinyar ta ƙi bayyana abin da ya faru da ita, amma daga baya ta zargi ’yan’uwan biyu da yi mata fyade.

Sai dai waɗanda ake zargin sun amince cewa sun yi jima’i da ita, amma sun yi ikirarin cewa ba su tilasta mata ba.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Delta, Bright Edafe, ya tabbatar da faruwar lamarin.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *