Wasu mazauna yankin ƙaramar hukumar Alimoshon jihar Legas, na bayyana damuwa da yadda  rashin kwashe shara akan lokaci ke shafar tasirin shirin tsaftar muhalli na wata-wata.

Al’ummar sun ce suna fitowa domin tsaftace muhallansu, kamfanonin kwashe shara ba sa zuwa kan lokaci, lamarin da ke sa ruwan sama da masu jari bola sake baza sharar.

Sai dai wasu mazauna yankin sun ce bai kamata a daina tsaftace muhalli ba saboda matsalar kwashe shara, duk da cewa tsafta nauyi ne da ya rataya a wuyan kowa domin kare lafiya.

A cikin watan Afrilun shekarar 2026 ne gwamnatin Jihar Lagos ta dawo da shirin tsaftar muhalli na wata-wata, inda ake taƙaita zirga-zirga daga ƙarfe 6:30 na safe zuwa 8:30 na hantsi a ranakun Asabar na ƙarshe wata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *