Wani abin fashewa da ake zargi bam ne ya fashe jiya a ƙarƙashin wata mota da aka ajiye a yankin Oke Mushin na Legas.

Lamarin ya jikkata mai motar kuma ya haddasa firgici a tsakanin mazauna yankin.

Fashewar ta sa hukumomin tsaro, ciki har da ƙwararru kan nakiyar bama-bamai da manyan jami’an ‘yan sanda, suka gaggauta zuwa wurin inda suka killace yankin tare da fara bincike.

Da yake jawabi a wurin da lamarin ya faru, Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Legas, CP Tijani Fatai, ya tabbatar da cewa binciken farko ya nuna an dasa na’urar fashewar ne a ƙarƙashin motar.

“Abin da ya fashe an tabbatar da cewa bam ne na zamani, IED. Mai motar ya samu ƙananan raunuka kuma an kai shi asibiti don jinya,” in ji shi.

“An kwaso ragowar IED ɗin kuma an kai su domin yin binciken kimiyya. An tabbatar da cewa yankin na cikin aminci a yanzu, kuma babu wani sauran fargaba ko tsoro,” in ji Fatai.

Kwamishinan ‘yan sandan ya buƙaci mazauna yankin da su kwantar da hankalinsu su ci gaba da harkokinsu na yau da kullum, inda ya ce hukumomin tsaro na kan lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *