Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ayyana kawo ƙarshen matsalar ruwa a wasu garuruwan da ke kewaye da Babban Birnin Tarayya Abuja (FCT).
Shugaban ya bayyan hakane yayin ƙaddamar da tsarin samar da ruwan sha ga al’ummomin Karu, Orozo, Jikwoyi, Kurudu da sauran yankunan da ke maƙwabtaka da su
Shugaban, wanda Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya wakilta, ya ce wannan aiki na nuna ƙudirin Ajandar Sabon Fata (Renewed Hope Agenda) wajen samar da muhimman ayyuka da hidimomi, kare martabar jama’a da kuma inganta rayuwar ‘yan Najeriya
- ‘Yan sanda sun tabbatar da kashe mutane 20 a sabon hari a Filato
- Fadar Shugaban Ƙasa da ɗan Majalisa sun yi watsi da kiran Tinubu ya yi murabus
- Kwamishinan ’yan sandan Abuja ya bai wa DPOs wa’adin mako biyu sukawo arshen fashi a tsakiyar birnin Abuja
A cewarsa, an yanke shawarar aiwatar da aikin ne bayan wani umarni da aka bayar bayan ƙaddamar da Babban Aikin Samar da Ruwan Sha na Abuja (Greater Abuja Water Supply Project), wanda ya tanadi cewa dole ne a faɗaɗa hanyoyin samar da ruwa zuwa garuruwan da ke wajen tsakiyar birnin
Tinubu ya bayyana cewa lokacin da Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya gabatar da ƙudirin Aikin Samar da Ruwa na Karu, gwamnatin tarayya ta amince da shi ba tare da ɓata lokaci ba saboda muhimmancinsa ga lafiyar jama’a da bunƙasar tattalin arziki.
