Rundunar ‘yan sandan Jihar Filato ta tabbatar da kashe mutane 20 a wani hari da aka kai ƙauyen Kawel, dake gundumar Mushere, a ƙaramar hukumar Bokkos, a safiyar ranar Lahadi, 21 ga Yuni 2026, yayin wani hari da wasu ‘yan bindiga suka kai. 

Rundunar, a wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin ta bakin Jami’in hulɗa da jama’a, PPRO, SP Alfred Alabo, ta bayyana cewa an tabbatar da mutuwar mutane goma sha takwas (18) a wurin da aka kai harin, yayin da aka garzaya da wasu uku (3) asibiti don kula da lafiyarsu.

‘Yan sandan sun ƙara da cewa daga baya, likita ya tabbatar da mutuwar biyu (2) daga cikin waɗanda suka jikkata, wanda ya kawo adadin waɗanda suka mutu zuwa ashirin (20).

Rundunar ‘Yan sandan ta ce an miƙa gawawwakin waɗanda suka mutu ga iyalansu domin binne su, yayin da iyalai suka ƙi a gudanar da bincike kan gawarwakin.

Yayin da take Allah wadai da faruwar lamarin, rundunar ta mika ta’aziyya ga iyalan mamatan da kuma al’ummar ƙaramar hukumar Bokkos masu son zaman lafiya bisa wannan mummunan lamari.

Ta kuma tabbatar wa jama’a cewa rundunar, tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro, za ta ci gaba da tura dukkan jami’an da suka dace don tabbatar da an gano waɗanda suka aikata wannan aika-aika, da kuma kama su, da gurfanar da su a gaban ƙuliya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *