Lionel Messi ya zama wanda ya fi kowa zura ƙwallaye a tarihin gasar cin kofin duniya bayan da kwallayensa biyu suka bai wa Argentina nasara da ci 2-0 kan Austria a Dallas.
A halin yanzu, Argentina ta tsallake zuwa zagaye na biyu kuma tana dab da tabbatar da zama ta ɗaya a rukunin J, matsayin da za a tabbatar idan Jordan ta kasa doke Algeria.
- Gasar Kofin Duniya: Magoya bayan Japan na cigaba da tsaftace Filin wasa
- Serena Williams za ta dawo gasar Wimbledon
Gaba ɗaya, Messi yana da ƙwallaye 18 a wasanni 28 na gasar cin kofin duniya, wanda ya sa ya ba Miroslav Klose tazarar ƙwallaye biyu a jerin masu zura ƙwallaye a gasar.
Messi, wand ya lashe kyautar Ballon d’Or sau takwas, ya kuma zama ɗan wasa na uku a tarihin gasar cin kofin duniya da ya zura ƙwallo a wasanni shida a jere, inda ya kamo Fontaine na Faransa a 1958 da Jairzinho na Brazil a 1970.