Gwarzuwa a wasan tennis, Serena Williams, wacce ta dawo wasa bayan shekaru huɗu za ta fafata a gasar mata ta Wimbledon, kamar yadda masu shirya gasar suka sanar a ranar Lahadi.
Williams, mai shekara 44, ta samu gurbi na ƙarshe da aka baiwa baƙi na musamman kafin fara gasar da za a fara wannan makon. Wannan zai zama gasar ta ta farko ta Grand Slam a fagen mata tun bayan US Open na shekarar 2022.
Williams da ‘yar uwarta Venus sun shirya fafatawa a Wimbledon a wasan mutum bib-biyu, inda za su sake haduwa a matsayin ƙungiya a karon farko tun 2016.
Serena da ‘yar uwarta Venus suna daga cikin ‘yan wasan tennis mata da suka fi kowa nasara a tarihi.
Kofunan Grand Slam 23 da Serena ta lashe, sune na biyu mafi yawa a tarihin gasar.
Wimbledon na daga cikin gasar da ta fi kwarewa, inda ta lashe kofuna 7 na gasar a Landan.
Venus da Serena sun lashe kofunan Grand Slam na bib-biyu sau 14, ciki har da guda 6 a gasar Wimbledon.
