Mataimakan Shugaban Ƙasa kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga da Dada Olusegun, tare da ɗan Majalisar Wakilai Philip Agbese, sun yi watsi da kiran da aka yi wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya yi murabus saboda matsalolin tattalin arziki da rashin tsaro.
Wannan kira ya fito ne daga Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Nigerian Democratic Congress, da kuma shugaban marasa rinjaye a Majalisar Wakilai, Fred Agbedi.
Fadar Shugaban Ƙasa, ta hannun Bayo Onanuga, ta bayyana bukatar Obi a matsayin “maras tushe”, kuma wata hanya ce ta karkatar da hankali daga nasarorin da gwamnati ta samu a fannoni daban-daban.
Onanuga ya ce nasarorin da jam’iyyar APC ta samu a zabukan baya-bayan nan a jihohin Ekiti, Nasarawa, Enugu, Ondo da Rivers sun nuna cewa jama’a har yanzu suna goyon bayan Shugaba Tinubu da jam’iyyarsa.
Ya kara da cewa:“Peter Obi ya kamata ya jira zaben shugaban ƙasa na 2027 idan yana son gwada farin jinin Tinubu, maimakon amfani da kafafen sada zumunta wajen matsa lamba ga shugaban da aka zaɓa.”
Onanuga, ya ce kwatanta tsarin siyasar Najeriya da na Birtaniya kuskure ne, domin Najeriya na amfani da tsarin shugaban ƙasa wanda kundin tsarin mulki ya tanadar masa wa’adin shekaru huɗu.
Ya ce gwamnatin Tinubu ta gaji tattalin arzikin da ke fama da matsaloli da dama kamar tallafin man fetur da ba zai dore ba, tsarin canjin kuɗi iri-iri, raguwar samar da ɗanyen mai da matsin lamba a harkokin kuɗi
A nasa bangaren, Dada Olusegun ya ce tsarin Firaminista na Birtaniya ya bambanta da tsarin shugaban ƙasa na Najeriya.
- Gasar Kofin Duniya: Magoya bayan Japan na cigaba da tsaftace Filin wasa
- Shugaba Tinubu ya naɗa Farfesa Oluwatoyin a matsayin shugaban Hukumar NUC
- Shugaban WhatsApp Will Cathcart ya sauka daga mukaminsa
Olusegun ya kuma yi nuni da cewa gwamnan Jihar Anambra, Charles Soludo, ya yaba da manufofin tattalin arzikin Tinubu, yana mai cewa sun taimaka wajen ceto tattalin arzikin ƙasa daga durƙushewa.
A Majalisar Wakilai ma, an samu sabani kan batun murabus din Tinubu.
Shugaban marasa rinjaye, Fred Agbedi, ya bukaci shugaban ƙasar ya magance matsalolin tsaro da tattalin arziki ko kuma ya sauka daga mulki.
Sai dai Philip Agbese, ɗan majalisar jam’iyyar Labour Party daga mazabar Ado/Okpokwu/Ogbadibo ta Jihar Benue, ya yi watsi da wannan kira. Ya ce wasu ‘yan siyasa ne ke amfani da lamarin domin shirye-shiryen zaben 2027.
Ya ce:“Kiran da ake yi wa Shugaba Tinubu ya yi murabus ba daga kishin ƙasa ya fito ba. Wata makarkashiya ce ta wasu ‘yan siyasa da ke son kawar da shi daga mulki ta kowace hanya.”
Agbese ya jaddada cewa magance rashin tsaro na buƙatar haɗin kan dukkan ‘yan Najeriya da tallafawa jami’an tsaro maimakon amfani da lamarin wajen siyasa.
