Ƙasar Israila da Lebanon sun amince da sabon tsarin yarjejeniya bayan tattaunawa mai tsawo na kwanaki huɗu a Washington, DC, da Amurka ta shiga tsakani, domin ƙoƙarin kawo ƙarshen rikicin da ya shafe watanni.

Isra’ila na ci gaba da mamaye kusan kashi 20 cikin 100 na yankin kudancin Lebanon, sannan rahotanni sun nuna cewa ta ƙashe sama da mutane 4,000 tun bayan da rikici ya ɓarke a ranar 2 ga Maris.

A baya an taba cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Nuwamba 2024, amma Isra’ila ta ci gaba da kai hare-hare kusan kullum tare da kin janye sojojinta, abin da ake ganin ya sabawa yarjejeniyar.

Sai dai sabuwar yarjejeniyar ba ta bayyana kai tsaye cewa Isra’ila za ta janye sojojinta ba.

Maimakon haka, ta danganta hakan ne da batun kwance damarar ƙungiyar Hezbollah — wani sharai da ƙungiyar ta sha ƙin amincewa da shi, tana mai cewa ba za ta mika makamanta ba.

Shugaban Hezbollah Naim Qassem ya yi watsi da wannan tsarin a ranar Asabar, inda ya bayyana shi a matsayin mara inganci kuma ba shi da ƙima.

Ƙungiyar ta Hezbollah ta kuma dage cewa dole ne Isra’ila ta fara janye sojojinta daga yankunan da ta mamaye kafin a tattauna wani abu.

A ranar Juma’a da yamma, magoya bayan Hezbollah sun cika titunan birnin Beirut domin nuna adawa da wannan yarjejeniya.

Abin jira a gani shine ko yarjejeniyar zata hanyar da da mai ido ko kuma a’a.

.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *