Dubban baƘin haure daga ƙasashen Afirka suna fuskantar rayuwa cikin fargaba bayan sake barkewar hare-haren Ƙyamar baƙi (xenophobia) a sassa daban-daban na Afirka ta Kudu, lamarin da ya tilasta wa mutane da dama barin gidajensu da kasuwancinsu da dukiyoyinsu domin neman tsira.
Wannan sabon rikici ya zo ne bayan shekaru da dama da baƙin haure suka shafe suna sake gina rayuwarsu bayan hare-haren makamantan haka da suka afku a shekarun 2008 da 2015 da 2019 waɗanda suka yi sanadin mutuwar mutane da dama tare da raba dubban mutane da matsugunusu.
Rahotanni sun nuna cewa wata kungiyar masu adawa da baƙin haure mai suna ( March da March) ta jagoranci zanga-zanga a wasu yankuna tana neman baƙin haure marasa takardu su fice daga ƙasar kafin ranar 30 ga Yuni, duk da cewa kungiyar ta musanta zargin ƙyamar baƙi, zanga-zangar da take yi na yawan kasancewa tare da hare-hare kan gidaje da shagunan baƙin haure.
A cikin watannin baya-bayan nan, an samu rahotannin kashe mutane akalla biyar musamman ‘yan ƙasar Mozambique, yayin da aka kona gidajen su tare da lalata shaguna da kuma tilastawa dubban mutane guduwa daga wuraren zamansu.
- Gwamnatin Tarayya ta gano tarin ma’adanai masu daraja a Jihar Kaduna
- Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026: Afirka ta Kudu, Morocco sun kai zagaye na 3
Saboda tsananin tashin hankali, gwamnatocin ƙasashen, Ghana da Najeriya da Malawi da Mozambique sun fara shirye-shiryen mayar da wasu daga cikin ‘yan ƙasar sun koma gida domin kare rayukansu.
Manema labarai su ruwaito cewa ɗaruruwan ‘yan Najeriya sun riga sun dawo gida bayan fuskantar hare-hare da tsangwama.
Sai dai da yawa daga cikinsu sun tarar da matsalolin tattalin arziki da rashin aikin yi irin waɗanda suka sa suka bar Najeriya tun farko.
Masana sun ce matsanancin talauci, rashin aikin yi da gazawar ayyukan gwamnati ne suka sa wasu ‘yan Afirka ta Kudu ke ɗora laifin matsalolin tattalin arziki kan ɓakin haure.
Ana kuma zargin wasu ‘yan siyasa da amfani da batun ba ƙ in haure domin samun goyon bayan jama’a kafin zabuka.
Afirka ta Kudu na daga cikin ƙasashen da suka fi karfin tattalin arziki a nahiyar, abin da ya sa miliyoyin mutane daga ƙasashe maƙwabta ke zuwa domin neman aiki da rayuwa mafi kyau Sai dai yawan rashin aikin yi da matsin tattalin arziki na ƙara haddasa rashin jituwa tsakanin wasu ‘yan ƙasa da baƙin haure.
Shugaban Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, ya yi Allah wadai da hare-haren, yana mai cewa gwamnati za ta ɗauki tsauraran matakai kan ƙungiyoyin da ke tayar da fitina da haddasa tashin hankali, Ya jaddada cewa aiwatar da dokokin shige da fice haƙƙin gwamnati ne kawai, ba na ƙkungiyoyin sa-kai ko masu ɗaukar doka a hannunsu ba.
Ya kuma bayyana cewa ba ƙ in haure ba su ne musabbabin talauci da rashin aikin yi ba, yana mai cewa waɗannan matsaloli sun samo asali ne daga Ƙalubalen tattalin arziki da Ƙasar ke fuskanta.
Yayin da wa’adin ranar 30 ga Yuni da masu zanga-zangar suka sanya ke ƙara matsowa ƙungiyoyin kare hƙn ɗan Adam da kungiyoyin ƙwadago suna gargaɗin cewa ƙasar na iya fuskantar ƙarin tashin hankali idan ba a ɗauki matakan dakile rikicin ba