Kasashen Afirka ta Kudu da Moroko sun kasance kan gaba cikin jerin kasashen nahiyar Afirka da suka fara tsallakawa zuwa zagayen ƙasashe 32 na gasar cin kofin duniya ta 2026.
A ranar laraba, Afirka ta Kudu ta lallasa Koriya ta Kudu da ci 1-0, domin samun gurbi a zagaye na gaba na gasar.
Ƙwallon Thapelo Maseko da ya zura a minti na 63 ta tabbatar da nasarar Bafana Bafana kan Koriya ta Kudu.
-
Gasar Cin Kofin Duniya 2026: Bafana Bafana ta kafa tarihi
-
An ci gaba da girmama Lionel Messi da manyan abubuwan tunawa da shi
A gefe guda kuma, ƙwallaye biyu da aka zura a ƙarshen wasa sun baiwa Moroko nasara mai wahala da ci 4-2 kan Haiti a wasansu na ƙarshe na Rukunin C a Gasar Cin Kofin Duniya, wanda ya sa suka kammala a matsayi na biyu.
‘Yan wasannin da suka zura ma Moroko kwallaye sun haɗa da Kyaftin din tawagar, Achraf Hakimi, Ismael Saibari, Soufiane Rahimi da kuma Gessime Yassine.