Kaɗan ne daga cikin ƴan wasan ƙwallon ƙafa da suka samu yabo da girmamawa kamar Lionel Messi. Duk da haka, masoyansa na ci gaba da ƙirƙiro sabbin hanyoyi na nuna girmamawa ga bajintarsa da kuma tasirin da ya yi a duniyar ƙwallon ƙafa.
Messi ya cika shekara 39 a ranar Laraba, kwanaki biyu kacal bayan ya sake kafa wani sabon tarihi a rayuwarsa ta wasa. Tauraron ɗan ƙasar Argentina ya zama wanda ya fi kowa zura ƙwallaye a tarihin gasar cin kofin duniya ta FIFA, bayan ya ci ƙwallaye na 17 da na 18 a gasar yayin da Argentina ta doke tawagar ƙasar Austria da ci 2–0. Hakan ya sa ya haura tarihin da Miroslav Klose ya riƙe a baya.
A cewar rahoton ESPN, girmamawar da ake yi wa Messi a Argentina ta kai wani sabon matsayi. A garin Cutral Co da ke yankin Patagonia, wasu masu fasaha sun buɗe wani mutum-mutumi mai tsawon ƙafa 85 (mita 26) na kyaftin ɗin da ya lashe Kofin Duniya. Wannan ya zama ɗaya daga cikin manyan abubuwan tunawa da aka taɓa ginawa domin girmama fitaccen ɗan wasan.
An gina mutum-mutumin da kusan tan 70 na ƙarfe, kuma cikin ɗan lokaci ya zama wurin da jama’a ke kai ziyara, duk da cewa akwai muhawara kan yadda kamanninsa suka yi kama da Messi.
- Majalisar Tarayya ta sake tsawaita aiwatar da kasafin 2025 zuwa Satumba
- Ku mai da sukar mutane tushen nasararku – Ali Nuhu
- Ƙudirin kafa ƴan sandan jihohi ya samu sabon ci gaba, bayan da Majalisar Dattawa ta amince da shi.
Wannan ƙaddamarwa ta zo ne watanni bayan wani babban mutum-mutumin Messi ya ja hankalin jama’a a yankin West Bengal na ƙasar India lokacin da tauraron ya kai ziyarar talla tare da takwarorinsa na ƙungiyar Inter Miami CF, ciki har da Luis Suárez da Rodrigo De Paul.
Wancan mutum-mutumin mai tsawon ƙafa 70 an yi masa kirari a lokacin a matsayin mafi girman mutum-mutumin ɗan wasan ƙwallon ƙafa a duniya. Sai dai daga baya an cire shi bayan jami’ai sun nuna damuwa kan lafiyarsa da tsaronsa.Yayin da ake cewa jami’ai a India sun yi tunanin mayar da mutum-mutumin zuwa wani wuri tare da sake girka shi, Argentina ta sake ɗaukar hankalin duniya da wani mutum-mutumi mafi girma kusa da ƙasar Messi.
Garin Cutral Co, wanda aka fi sani da harkar haƙar mai fiye da yawon buɗe ido, ya samu ƙaruwa sosai a yawan baƙi tun bayan ƙaddamar da mutum-mutumin a ranar 16 ga Yuni, domin ya zo daidai da wasan farko na Argentina a gasar 2026 FIFA World Cup.
Wanda ya ƙera wannan babban mutum-mutumi shi ne mai fasaha mai shekara 61, Aldo Beroisa. Ya shafe watanni 18 yana aikin kammala shi. Beroisa ya shahara wajen ƙera manyan mutum-mutuman dinosaur da kuma na fitattun mutane a tarihin Argentina, kuma ya ce mutum-mutumin Messi yana da muhimmanci ta musamman a gare shi.