Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Olatunji Rilwan Disu, ya tura Mataimakin Sufeto Janar na ’Yan Sanda mai kula da Hedikwatar rundunar a shiyya ta 4 da ke Makurdi, Dankombo F. Morris, zuwa Jihar Filato domin gudanar da ziyarar tantance yanayin tsaro bayan hare-haren da aka kai a Ƙaramar Hukumar Bokkos.

A yayin ziyarar da ya kai ranar 23 ga watan Yunin 2026, AIG Morris ya gana da shugabannin al’umma da sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki domin tantance halin da ake ciki da kuma ƙarfafa ƙoƙarin dawo da zaman lafiya a yankunan da abin ya shafa.

Ya ce rundunar na ɗaukar dukkan matakan da doka ta tanada domin kamo masu hannu a hare-haren da kuma hana sake aukuwar irin waɗannan hare-hare a gaba.

AIG Morris ya kuma bayyana cewa bisa umarnin Sufeto Janar na ’Yan Sanda, an tura ƙarin jami’ai da kayan aikin tsaro zuwa Jihar Filato, musamman yankunan da abin ya shafa a Ƙaramar Hukumar Bokkos, domin ƙarfafa ayyukan tsaro, ƙara yawan jami’ai a yankin da kuma tallafa wa ƙoƙarin dawo da zaman lafiya.

Ya buƙaci mazauna yankin su kasance masu bin doka da oda tare da kauce wa ɗaukar matakan ramuwar gayya da ka iya kawo cikas ga ƙoƙarin samar da zaman lafiya da tsaro.

Da yake isar da saƙon ta’aziyyar Sufeto Janar na ’Yan Sanda da tawagar jagorancin rundunar, AIG Morris ya jajanta wa iyalan waɗanda hare-haren suka shafa, tare da tabbatar wa mazauna yankin cewa rundunar ’yan sanda za ta ci gaba da ƙoƙarin tabbatar da an kamo waɗanda ake zargi da hannu a hare-haren domin gurfanar da su a gaban kuliya.

Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya ta ce za ta ci gaba da aiki tare da masu ruwa da tsaki da sauran hukumomin tsaro domin kare rayuka da dukiyoyi da tabbatar da tsaron jama’a da kuma tallafa wa samar da ɗorewar zaman lafiya a Jihar Filato da ƙasa baki ɗaya.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *