Rundunar ’Yan Sandan Najeriya (NPF) ta yi watsi da wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, wanda ke zargin cewa an ga wani ɗan sanda cikin mu’amala da ’yan bindiga a Jihar Katsina.

Wata sanarwa da Jami’in hulɗa da Jama’a na Rundunar CSP Anietie Okokon Edem Iniedu ya fitar, yace mutanen da aka gani a cikin bidiyon ba ’yan bindiga ba ne, su mambobi ne da aka amince da su na Kungiyar Masu Tsaro ta Sa-kai ta Najeriya (Vigilante Group of Nigeria – VGN) da kuma mafarauta masu rijista, waɗanda ke taimakawa ayyukan tsaro tare da hukumomin tsaro a ƙananan hukumomin Musawa da Matazu na Jihar Katsina.

Rundunar ’YanSandan ta yi Allah-wadai da bidiyon da ta kira wanda ke karkatar da gaskiya da kuma yaɗa bayanan ƙarya da ka iya haifar da fargaba a tsakanin jama’a, dama rage amincewa da hukumomin tsaro, da kuma kawo cikas ga ayyukan tsaro da ake gudanarwa.

Sanarwar ta shawarci jama’a da su yi watsi da iƙirarin ƙarya da aka haɗa da bidiyon, tare da dogaro kawai da bayanan da Rundunar ’YanSandan da sauran hukumomin gwamnati da aka ba izini ke fitarwa.

Rundunar ta yi gargaɗi ga duk wani mutum ko ƙungiya da ke ƙirƙira ko wallafawa ko yaɗa bayanan ƙarya da za su iya kawo cikas ga zaman lafiya da tsaro da su daina nan take, domin ana iya ɗaukar matakin doka a kansu.

Rundunar ’Yan Sandan Najeriya na ci gaba da jajircewa wajen aiki tare da halastattun masu ruwa da tsaki na tsaron al’umma da sauran abokan hulɗa domin kare rayuka, tabbatar da tsaron al’umma, da yaƙi da aikata laifuka a faɗin ƙasar nan

Bidiyon da ake yaɗawa a shafukan sada zumunta ya nuna wata mu’amala ta yau da kullum tsakanin wani ɗan sanda da masu sa-kai na tsaro,  yayin da suke tafiya zuwa wani yanki da aka ware domin gudanar da aiki, a ƙoƙarin yaƙi da aikata laifuka da kuma ƙarfafa tsaron jama’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *