Wani gini mai hawa uku da ake ginawa ya rufta a Fatakwal, babban birnin Jihar Rivers.
Lamarin ya faru ne ranar Laraba a bayan Gidan Mai na Eternal, daura da titin Chief Sam Ngbor, daga kan babbar hanyar Peter Odili.
An ruwaito cewa ma’aikatan gini suna wurin aikin lokacin da ginin ya faɗi, inda ya danne wasu daga cikinsu a ƙarƙashin baraguzan ginin.
Mazauna yankin da suka yi magana da jaridar Daily Trust sun ce ma’aikata da dama sun makale a ƙarƙashin baraguzan ginin, inda su kayi kira da a gaggauta kai ɗaukin gaggawa.
Jami’an hukumomin da abin ya shafa sun isa wurin da abin ya faru jim kaɗan bayan faruwar lamarin kuma sun fara aikin ceto.
Ko da yake ba a tabbatar da mutuwar kowa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto, kazalika ba a san abin da ya jawo ruftawar ginin ba.
Gwamnatin Jihar Rivers har yanzu ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Rivers, ASP Blessing Kaborlo Agabe, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce an ceto mutane biyu kuma an kai su asibiti.
Ta ƙara da cewa ana ci gaba da aikin ceto don tantance ko akwai wasu mutane da ke maƙale a cikin baraguzan.