Faransa ta tabbatar da samun mutum na farko da ya kamu da cutar Ebola a cikin ƙasar tun bayan barkewar cutar

Wani likita da ya dawo daga aikin agaji a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo aka tabbatar yana ɗauke da cutar.

A cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Lafiya ta Faransa ta fitar ranar Laraba, ta ce ma’aikacin lafiyar yana aiki ne a ɗaya daga cikin yankunan da cutar ke yaduwa.

“An kwantar da mara lafiyar a wani babban asibiti na musamman, inda ake kula da shi bisa tsauraran matakan kariya da kula da cututtuka masu haɗari,” in ji ma’aikatar.

Sanarwar ta ƙara da cewa  an aiwatar da dukkan matakan kariya da suka dace, ciki har da killace mara lafiyar tun lokacin da ya iso Faransa, sannan aka kai shi asibiti cikin tsaro domin hana duk wani yiwuwar yaduwar cutar.

A halin yanzu ana gudanar da binciken gano mutanen da suka yi hulɗa da mara lafiyar Hukumomin lafiya za su tuntube su tare da umartar su su killace kansu na tsawon kwanaki 21, in ji sanarwar.

Tun daga watan Mayu, lardin Ituri da ke arewa maso gabashin DRC ya kasance cibiyar barkewar cutar Ebola, wadda ta yi sanadin mutuwar fiye da mutum 260 tare da kamuwa da sama da mutum 1,000 a ƙasar ta tsakiyar Afirka.

An kuma samu rahoton bullar cutar a maƙwabciyar ƙasar Uganda.

A ranar 17 ga Mayu, Ƙungiyar lafiya ta majalisar Dinkin Duniya (WHO) ta ayyana barkewar cutar a matsayin “gaggawar lafiyar jama’a ta duniya”.

Yawancin barkewar cutar Ebola da aka samu a DRC a baya bayan nan sun samo asali ne daga nau’in ƙwayar cutar da ake kira Ebola Zaire, amma wannan barkewar ta samo asali ne daga wani nau’i daban mai suna Bundibugyo, wanda a halin yanzu babu wata rigakafi ko magani da aka amince da shi a hukumance domin magance shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *