Jamhuriyar Nijar ta miƙa buƙatarta a hukumance na ficewa daga Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya (ICC), kamar yadda kotun wacce ke da zama a Hogue ta sanar a ranar Talata.
Kotun ta bayyana cewa Kasar Nijar ta sanar da matakin ne watanni tara baya tare da ƙawayenta Mali da Burkina Faso.
Ƙasashen uku na Sahel duk gwamnatocin sojoji ne ke mulkinsu waɗanda suka hau mulki ta hanyar juyin mulki tsakanin 2020 da 2023.
-
Andy Burnham na ƙara kusantar kujerar Firayiministan Birtaniya
-
Gwamnatin Burkina Faso ta haramta wa wasu malaman addinin Musulunci wa’azi.
A cikin wata sanarwa da aka aika wa Kamfanin dillancin Labaran AFP ranar Talata, ICC ta ce ta karɓi “takardar ficewa” ranar 18 ga Yuni daga Nijar, wadda Janar Abdourahamane Tiani ke jagoranta.
Buƙatar za ta fara aiki ne a ranar 18 ga Yuni, 2027 shekara ɗaya bayan sanarwar, in ji kotun.
An kafa Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya a 2002, kuma aikinta shi ne gurfanar da masu aikata manyan laifuka, irin su laifukan yaƙi.
ICC tana da ƙasashe mambobi 125 a halin yanzu.
Amurka da Rasha ba sa cikinsu, haka ma Isra’ila da Sin da Myanmar.