Gwamnatin gabashin Libya ta sanar da haramta wa ‘yan ƙasashen Sudan, Eritrea, Habasha da Somaliya shiga ƙasar ta dukkan hanyoyin ƙasa da ruwa da iska a wani mataki na dakile yawaitar baƙin hauren da ke bi ta Libya zuwa nahiyar Turai.
Gwamnatin Osama Hamad mai hedikwata a Benghazi ta ce dokar ba za ta shafi jami’an diflomasiyya da ma’aikatan sassan lafiya da ilimi ba.
Wannan gwamnati na samun goyon bayan kwamandan soji Khalifa Haftar, wanda ke iko da gabashin Libya da kuma manyan sassan kudancin kasar.
Sanarwar ta zo ne yayin da ake ci gaba da gano gawarwakin baƙin haure da suka mutu bayan kifewar wani jirgin ruwa a gabar tekun gabashin Libya a makon da ya gabata.
- MDD ta ce janye tallafin yaƙi da cutar ƙanjamau na Amurka ga Afirka Ta Kudu illa ne
- An yanke wa ƴan fashi da makami uku hukuncin kisa
Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da baƙin haure da ‘yan gudun hijira dubu ɗari tara ne ke zaune a Libya, inda ‘yan Sudan suka fi yawa.
Da dama daga cikinsu na ƙoƙarin isa Turai ta hanyar tsallaka Tekun Bahar Rum, amma sau da yawa hukumomi kan tare jiragensu tare da mayar da su Libya.
Masu bincike na Majalisar Dinkin Duniya sun bayyana cewa wasu daga cikin baƙin hauren da ake mayarwa Libya na fuskantar tsarewa a cibiyoyin gwamnati, inda ake zargin suna fuskantar cin zarafi da suka haɗa da aikin dole, duka, fyade da azabtarwa.
Tun bayan kifar da gwamnatin tsohon shugaban ƙasar Moammar Gadhafi a shekarar 2011 da goyon bayan kungiyar NATO, Libya ke fama da rikice-rikicen siyasa da tsaro.
A yanzu haka ƙasar na da gwamnatoci biyu masu iko a yankuna daban-daban; ɗaya a Tripoli da ƙasashen duniya suka amince da ita, da kuma wata a gabashin ƙasar.