Ƙudirin kafa ƴan sandan jihohi da aka daɗe ana muhawara a kansa ya samu sabon ci gaba jiya, bayan da Majalisar Dattawa ta amince da shi.

Tun da farko, Majalisar Wakilai ta riga ta amince da kudirin mai taken: Ƙudirin Dokar Gyaran Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya na 1999 domin samar da Ƴan Sandan Jihohi da sauran abubuwan da suka shafe su (Gyara na Shida), 2026.”

Sai dai rahotanni sun nuna cewa har yanzu Majalisar Wakilai za ta daidaita abin da kudirinta ya kunsa da na kudirin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aika. Bayan haka ne za a sake tura shi zuwa Majalisar Dattawa domin ci gaba da matakan da suka dace.

A ranar Talata, shugaban ƙasa ya aika wa Majalisar Dattawa wasiƙa yana neman a gaggauta duba kudirin. Saboda haka, Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dattawa, Opeyemi Bamidele, ya gabatar da ƙudirin domin karatu na farko, na biyu da na uku.

Kafin a fara tattaunawa kan kudirin, Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, wanda ya jagoranci zaman, ya bayyana cewa idan an kammala amincewa da ƙudirin, za a tura shi zuwa majalisun dokoki na jihohi domin su ma su yi nazari da yanke hukunci a kansa.

Yayin da yake jagorantar muhawarar kudirin, Bamidele ya ce an shafe lokaci mai tsawo ana tattaunawa da masu ruwa da tsaki tare da yin cikakken nazari a majalisun dokokin biyu.

Ya ƙara da cewa, tsawon shekaru biyu da suka gabata ana tattauna wannan kudiri a sassa daban-daban na ƙasar nan ta hannun Kwamitin Gyaran Kundin Tsarin Mulki na Majalisar Dattawa, tare da karɓar shawarwari daga muhimman masu ruwa da tsaki.

A cewarsa, ƙudirin na neman: ci gaba da barin Ƴan Sandan Tarayya su kula da ayyukan tsaro na tarayya da kafa Ƴan Sandan Jihohi ga jihohin da suka zaɓi samar da su da samar da kariya a kundin tsarin mulki domin hana amfani da su ta hanyar da ba ta dace ba ko don manufofin siyasa  da  kafa Hukumar Kula da Ayyukan Ƴan Sandan Jihohi mai cin gashin kanta da kuma samar da mafi ƙarancin ƙa’idojin aikin ƴan sanda da za su shafi ƙasa baki ɗaya.

Har ila yau, ya ce kudirin zai Ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin ƴan sandan tarayya da na jihohi tare da Kare haƙƙoƙin ɗan Adam da ƴancin walwala na jama’a da kuma Samar da hanyoyin da gwamnatin tarayya za ta iya shiga tsakani a lokutan da tsaron jama’a ko tsaron ƙasa ya fuskanci barazana mai tsanani.

Rahotanni sun nuna cewa kafin ƙudirin ya wuce karatu na uku, mafi yawan sanatoci sun goyi bayan dukkan sashe 26 da ake son gyarawa.

Sun nuna amincewarsu ne ta hanyar ƙuri’ar murya lokacin da Akpabio ya gabatar da su ɗaya bayan ɗaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *