Jami’an Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati ta Najeriya (EFCC) shiyyar Abuja, sun kama wasu mutane 17 da ake zargi da aikata damfarar yanar gizo a ranar Talata, 17 ga Yuli, 2025.

An kama waɗanda ake zargin ne a yankin Mararaba da ke Jihar Nasarawa, bayan samun sahihan bayanan sirri da ke nuna cewa suna da hannu a ayyukan damfarar da suka shafi amfani da yanar gizo.

Kayan da aka ƙwato daga hannunsu sun haɗa da motoci biyar, wayoyin hannu 20 da kuma kwamfyutocin tafi-da-gidanka guda huɗu.

Hukumar tace da zarar ta kammala bincike za ta gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *