Bafana Bafana sun kafa wani sabon tarihi a gasar cin kofin duniya, inda ta samu gurbi a zagaye na gaba na kasashe 32 na gasar Cin Kofin Duniya ta 2026.
Kwallon Thapelo Maseko da ya zura a minti na 63 ta tabbatar da nasarar Bafana Bafana kan Koriya ta Kudu da ci 1-0 a wasan da suka fafata ranar Laraba.
-
An ci gaba da girmama Lionel Messi da manyan abubuwan tunawa da shi
-
Ronaldo ya zama ɗan wasa na farko da ya zura ƙwallo a gasar cin kofin duniya daban-daban har guda shida
Gwmanatin Afirka ta Kudu ta taya tawagar murnar wannan nasara, inda ta ce ‘yan wasan sun nuna jarumta da azama tare da sanya ƙasar alfahari a fagen duniya.
“Afirka ta Kudu ta haɗu wuri ɗaya cikin murnar wannan nasara.
Muna taya Bafana Bafana murna, tafiyar ta ci gaba!
