Dikko Raɗɗa - Gwamnan Jihar Katsina

Gwamnatin Jihar Katsina ta karyata zargin da aka yi cewa ta dauki nauyin aikin Hajji ga shugabannin ‘yan bindiga ko wasu da ke da hannu a ayyukan ta’addanci da sauran laifuka, tana mai bayyana zargin a matsayin ƙarya marar tushe da nufin yaudarar jama’a

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Kwamishinan Tsaron da Harkokin Cikin Gida na Jihar Katsina, Dakta Nasir Mua’azu, ya fitar a ranar 24 ga watan Yunin 2026.

Sanarwar ta zo ne a martani ga kalaman da wani mai suna Bashir Kurfi ya yi a wani shiri da aka watsa a Trust TV, inda ya yi zargin cewa gwamnatin jihar ta dauki nauyin aikin Hajji ga wasu shugabannin ‘yan bindiga.

Gwamnatin jihar ta bayyana cewa zargin ba shi da tushe ko makama, tare da jaddada cewa an yi shi ne da nufin karkatar da hankalin jama’a da kuma raunana ƙoƙarin da gwamnati da hukumomin tsaro ke yi wajen magance matsalolin tsaro a jihar.

A cewar sanarwar, abin takaici ne yadda ake yaɗa irin waɗannan zarge-zarge a daidai lokacin da hukumomin tsaro, tare da goyon bayan gwamnatin jihar, suka samu nasarori masu yawa a yaƙi da ‘yan bindiga da sauran masu aikata laifuka.

Gwamnatin ta kuma zargi wasu mutane da ƙungiyoyi da amfani da batun tsaro domin cimma muradunsu na siyasa da na kashin kai, tana mai cewa wasu daga cikinsu ba su ji daɗin yadda gwamnatin ta ƙi amincewa da wasu tsare-tsare da take zargin za su karkatar da kuɗaɗen jama’a daga ayyukan raya ƙasa da shirye-shiryen jin daɗin al’umma.

Sanarwar ta ƙalubalanci masu yaɗa zargin da su gabatar da sahihai kuma tabbatattun hujjoji da za su tabbatar da iƙirarinsu, tana mai gargaɗin cewa idan suka kasa yin hakan, gwamnati za ta yi amfani da hanyoyin doka domin kare martabarta da kuma ɗaukar mataki kan masu yaɗa bayanan ƙarya da ɓatanci.

Gwamnatin Jihar Katsina ta kuma yi kira ga jama’a da su yi watsi da waɗannan zarge-zarge, tare da ci gaba da bai wa hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki goyon baya wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a faɗin jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *