Gwamnatin Tarayya ta sanar da gano wani katafaren yankin ma’adanai masu tarin yawa a Jihar Kaduna, wanda ke ɗauke da ma’adanan dutsen platinum da zinariya da Farar Azurfa da jan ƙarfe da lithiyom da kuma wasu muhimman ma’adanai da ake kira ‘rare earth elements’, wato sindaran Ƙasa da ba a fiye samun su ba.
Ministan Albarkatun Ma’adinai, Dele Alake ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin buɗe Taron Zuba Jari kan Albarkatun Ƙasa da Makamashi na nahiyar Afirka na shekarar 2026 da aka gudanar a Abuja.
Ya ce Hukumar Binciken Ƙasa da Ma’adanai ta Nijeriya (NGSA) ce ta tabbatar da binciken bayan wani kamfani mai zaman kansa ya gudanar da ayyukan bincike tare da haɗin gwiwar hukumar.
A cewarsa, yankin da aka gano na ɗauke da ma’adanai masu inganci da daraja da ake buƙata sosai a duniya wajen samar da makamashi mai tsafta, masana’antu da sabbin fasahohi.
- Ba mu kai ‘yan bindiga aikin Hajji ba – Gwamnatin Katsina
- Gasar Cin Kofin Duniya 2026: Bafana Bafana ta kafa tarihi
- EFCC ta kama mutane 17 da ake zargi da damfara ta yanar gizo
Ya bayyana binciken a matsayin ɗaya daga cikin manyan nasarorin da aka samu a fannin haƙar ma’adanai a Nijeriya cikin ‘yan shekarun nan.
Ministan ya ce wannan ne karo na farko da gwamnati ke bayyana wannan bincike a hukumance, yana mai cewa hakan na nuna ci gaban da ake samu a ƙoƙarin gano sabbin ma’adanai a faɗin ƙasar.
Sanarwar ta zo ne a daidai lokacin da kamfanin Steron Mining and Company Limited ya bayyana cewa ya gano kimanin tan miliyan 3.3 na ma’adanin lithium a wurin haƙarsa da ke Abuja.
Alake ya ce gwamnatin Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, na aiwatar da sauye-sauye domin bunƙasa fannin ma’adanai, jawo jarin ƙasashen waje da samar da ayyukan yi.