Akalla mutum 32 ne suka mutu yayin da daruruwa suka jikkata sakamakon wasu manyan girgizar kasa guda biyu da suka afku a jere a ƙasar Venezuela, lamarin da ya haddasa rushewar gine-gine da dama a babban birnin ƙasar, Caracas.

Shugaban ƙasar mai rikon ƙwarya, Delcy Rodríguez, ta ayyana dokar ta-baci tare da sanar da rufe Filin Jiragen Sama na Simon Bolivar da ke Caracas saboda barnar da girgizar ta yi wa kayayyakin filin.

Hukumar Kula da Yanayin kasa ta Amurka (USGS) ta ce girgizar farko mai ƙarfin maki 7.2 ta auku ne a yammacin garin Morón, mai nisan kilomita 168 daga Caracas.

Hukumar ta ƙara da cewa minti guda bayan haka wata girgizar ƙasa ta biyu mai karfin maki 7.5 ta sake afkuwa a yankin.

USGS ta yi gargaɗin cewa akwai yiwuwar adadin waɗanda suka mutu da waɗanda suka jikkata ya ƙaru, tare da bayyana cewa bala’in na iya shafar sassa da dama na ƙasar.

Wata ‘yar jarida da ke Caracas, Noris Soto, ta ce mutane da dama sun rasa komai Sannan da dama suna cikin gidajensu lokacin da girgizar kasar ta afku domin ranar hutu ce a ƙasar.

Ta shaida cewa tana gida tare da iyalanta suna kallon gasar cin kofin duniya lokacin da suka fara jin ƙasa tana girgiza sosai.

“Mun ji wata irin girgiza mai karfi, sannan na ga gilasan tagogi sun farfashe. Ginin da nake ciki ya samu babbar tsaga a tsakiya,” in ji ta.

Ta ce mutane sun yi ta ƙoƙarin ficewa daga gidajensu domin tsira, yayin da firgici ya mamaye al’umma.

“Ba mu shirya wa irin wannan bala’i ba. Halin da ake ciki yana da matuƙar tsanani, kuma har yanzu mutane suna cikin ruɗani suna , ƙoƙarin fahimtar abin da ya faru,” ta , ƙara da cewa.

Soto ta ce mutane ba su da masaniyar yadda za su tunkari irin wannan yanayi, kasancewar girgizar , ƙasa ta karshe da ta taba afkawa Venezuela mai irin wannan karfi ta faru ne tun cikin shekarun 1960.

“Lokacin da ka ji  ƙasa tana motsi a ƙarkashinka, kana jin tsoro kuma ba ka da tabbacin abin da zai biyo baya. Abu ne mai firgitarwa ga kowa,” in ji ta.

Ta kuma bayyana cewa har yanzu ba a tantance cikakken girman barnar da bala’in ya yi ba, musamman saboda hanyoyin sadarwa da suka hada da layukan waya da intanet sun katse.

“Bayanan da muke samu kadan-kadan suna nuna cewa lamarin ya fi yadda ake zato muni,” in ji ta.

Ta ƙara da cewa mutane da yawa sun rasa gidajensu, yayin da wasu suka rasa kusan dukiyoyinsu baki ɗaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *