Jami’an tsaron Kenya sun baza ɗimbin jami’an ‘yan sanda a manyan tituna da muhimman wuraren a yau ranar Alhamis domin dakile zanga-zangar tunawa da cika shekaru biyu da fara gagarumar bore da matasan Gen Z suka jagoranta a shekarar 2024.
A watan Yunin a shekara ta 2024 ne dubban matasa suka mamaye titunan ƙasar suna zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa da matsin tattalin arziki da kuma cin hanci da rashawa, zanga-zangar ta kai kololuwar lokacin da masu zanga-zangar suka kutsa cikin ginin majalisar dokokin tarayya lamarin da ya tilastawa gwamnati janye sabbin harajin da take son kakkaba wa jama’ tun daga wannan lokacin ranar 25 ga Yuni ta zama ranar tunawa da gwagwarmayar matasa a Kenya, yayin da rashin jin daɗin jama’a da gwamnatin Shugaba William Ruto ke ci gaba da karuwa.
Sai dai wannan gwagwarmaya ta zo da babban farashi hukumar sa ido kan ayyukan ‘yan sanda ta bayyana cewa aƙalla mutane 127 ne suka rasa rayukansu a cikin shekaru biyun da suka gabata sakamakon zanga-zangar da tarzomar da ta biyo baya, masu fafutukar kare hakƙin ɗan Adam sun zargi jami’an tsaro da amfani da karfi fiye da kima, inda aka riƙa harbin masu zanga-zanga ba tare da fuskantar hukunci ba.
- Dubban baƙin haure na tserewa saboda sabuwar barkewar rikicin ƙyamar baƙi a Afirka ta Kudu.
- Girgizar ƙasa mai ƙarfi ta kashe mutum 32 tare da jikkata ɗaruruwa a Venezuela
A wani mahaɗar hanya a Nairobi, Kasim Ramadan mai shekaru 25 ya bayyana cewa shi da abokansa sun fito domin tunawa da waɗanda suka mutu a zanga-zangar shekara ta 2024 yayin da yace a yau ‘yan sanda sun fi yawa fiye da yadda muka saba gani tun kafin karfe takwas na safe sun fara harba mana barkonon tsohuwa amma ba mu tsorota ba, mun fito ne domin tunawa da waɗanda suka mutu a majalisar dokoki. A gefe guda kuma, Shugaba William Ruto ya ce kundin tsarin mulkin ƙasar ya bai wa jama’a damar yin zanga-zanga cikin lumana, amma ya gargadi waɗanda za su yi amfani da damar wajen lalata dukiyoyi ko tayar da tarzoma.
Yayin da zaben shugaban ƙasa nan gaba ke ƙara matsowa a watan Agustan 2027, masu lura da al’amuran siyasa na ganin cewa zanga-zangar Gen Z ta sauya yanayin siyasar Kenya, inda matasa ke ƙara nuna ƙarfin tasirinsu wajen neman sauyi, yaƙi da cin hanci da rashawa da kuma neman ingantacciyar rayuwa, sai dai abin da ke faruwa a yau ya nuna cewa har yanzu akwai babban giɓi tsakanin gwamnati da matasan ƙasar, kuma wannan na iya zama ɗaya daga cikin manyan batutuwan da za su mamaye siyasar Kenya kafin babban zaben shekara ta 2027.