Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Najeriya (NAFDAC) ta gargaɗi al’ummar ƙasar kan yaduwar wasu abubuwan sha masu kuzari da ke ɗauke da barasa, bayan da hukumomin Ghana suka ƙwace kimanin akwatuna 140 na irin waɗannan kayayyaki yayin wani samame na tabbatar da bin ƙa’idoji.
A cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na intanet, NAFDAC ta ce Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta Ghana (FDA) ce ta ƙwace kayayyakin a yankin kudancin ƙasar saboda damuwa kan lafiyarsu da kuma matsayin amincewar da aka ba su.
Hukumar ta bayyana cewa tun da farko an haramta sayarwa da rarraba wadannan kayayyaki saboda hadarin da ka iya tasowa daga hada barasa da sinadarai masu motsa jiki da ake samu a yawancin abubuwan sha masu kuzari.
-
Ba mu kai ‘yan bindiga aikin Hajji ba – Gwamnatin Katsina
-
Ba mu kai ‘yan bindiga aikin Hajji ba – Gwamnatin Katsina
NAFDAC ta ambaci sunayen kayayyakin da abin ya shafa da suka hada da Bel Ice Vodka Energy Drink, wanda kamfanin Bel Beverages na Ghana ke samarwa, da kuma Cody’s Vody Energy Mix, wanda kamfanin Jens Warneke Export da ke Bremen a Jamus ke ƙerawa.
Hukumar ta yi gargaɗin cewa irin waɗannan abubuwan sha na iya haifar da matsalolin lafiya, domin sinadaran da ke ƙunshe da su na iya rage fahimtar mutum game da tasirin maye, wanda hakan kan sa mai amfani ya kasa gane yadda barasar ta shafe shi.
A cewar NAFDAC, matasa da samari na cikin wadanda suka fi fuskantar hadarin shan barasa fiye da kima, yanke hukunci marar kyau, shiga halaye masu hadari da kuma matsalolin da suka shafi daidaiton motsi da tunani.
Haka kuma, hukumar ta ce amfani da irin wadannan kayayyaki na iya haifar da matsalolin zuciya da jijiyoyin jini, ciki har da saurin bugun zuciya da hauhawar jini.
Sanarwar ta ƙara da cewa, “Abubuwan sha masu kuzari da ke dauke da barasa na iya zama barazana ga lafiya saboda sinadaran motsa jiki da ke cikinsu na iya boye tasirin maye. Hakan na iya sa masu amfani su kasa gane yadda barasar ta shafe su.”
NAFDAC ta ce ta fara gudanar da sa ido a kasuwanni da kuma wasu ayyukan kulawa domin hana shigar da kayayyakin da ba a amince da su ba ko kuma waɗanda ka iya zama barazana ga lafiya cikin Najeriya.
Hukumar ta kuma yi gargadin cewa za ta dauki matakin doka kan duk wani mutum ko ƙungiya da aka samu na shigo da, rarrabawa ko sayar da wadannan kayayyaki.
Ta shawarci masu shigo da kaya, dillalai, masu sayar da kaya da kuma masu amfani da su da su tabbatar ba a shigo da, tallata ko sayar da abubuwan shan da abin ya shafa a Najeriya ba.
Haka kuma, NAFDAC ta buƙaci ’yan kasuwa su tabbatar duk abubuwan shan da suke sayarwa sun cika sharuɗɗan rajista da ƙa’idojin hukumar.
Ta kuma roƙi masu amfani da su da su kai rahoton duk inda suka ga wadannan kayayyaki ko kuma duk wata matsalar lafiya da ake zargin tana da alaƙa da amfani da su ga ofishin NAFDAC mafi kusa ko ta hanyoyin bayar da rahoto na intanet.
NAFDAC ta jaddada cewa za ta ci gaba da sanya ido domin kare lafiyar jama’a tare da hana kayayyakin da ba su da aminci shiga kasuwar Najeriya.
ɓ, ɗ, ƙ, ƴ · ɓ → Ɓ