Wani shahararren mai fafutukar siyasa da yaƙi da cin hanci da rashawa, Ibrahim Garba Wala (wanda ake kira IG Wala) ya kalubalanci masu sharhi kan al’amuran jama’a, da dukkan abokan gwagwarmaya daga kowane yanki da ke nuna damuwa game da yaran Nijeriya da su hada karfi wuri guda don tunkarar matsalar.

IG Wala ya yi Kalubalen nasa ne a cikin wata wasika da ya wallfa a shafinsa na facebook.

Ya ce tsawon makonni da dama, sararin yanar gizo ya cika da wata guguwa ta muhawara. An yi ta jefa zarge-zarge na gama-gari, an yi ta mayar da martani, kuma bidiyon nazari sun tara miliyoyin masu kallo dangane da halin da yaran Arewa ke ciki, zargin watsi da su, da kuma yadda suke cikin haɗarin rayuwar titi.

IG Wala ya ci gaba da cewa ‘amma yayin da ƙurar wannan cece-kucen ke lafa, haƙiƙanin rayuwa bai sauya ba. Yaran nan har yanzu suna kan titunan siminti na Kano, Kaduna, da sauran sassan yankuna, suna fafutukar rayuwa cikin yunwa’, yana mai karawa da cewa guguwar yanar gizo ba za ta ciyar da su ba, ba kuma za ta tabbatar da makomarsu ba.

Ya ce ‘idan da gaske muna damuwa da su, idan hawayen da aka zubar a gaban kyamara da fushin da aka rubuta a sassan sharhi na gaskiya ne, to lokaci ya yi da za mu fita daga hayaniyar cece-kuce zuwa ga aikin gina mafita mai ɗorewa da ke kawo sauyi a tsarin rayuwa’.

IG Wala ya ce yana miƙa ƙalubale kai tsaye ga VDM da dukkan abokan gwagwarmaya daga Kudu da Arewa waɗanda ke cewa suna da ruwa da tsaki a makomar waɗannan yara. Ku daina yawan magana. Ku daina bidiyoyi. Ku zo filin aiki, mu gwada ƙudurinmu ta hanyar shirinSave Arewa Child (SAC).

Wasikar ta ƙara da cewa shirin SAC ba wata ƙungiyar agaji ce ta manyan masu mulki da ke neman tallafin ƙasashen waje ba, tsari ne na aiki daga tushe, wanda ke amfani da bayanai da hujjoji, domin haɗa tsarin shugabancin gargajiya na Arewa da hanyoyin gudanarwa na zamani tare da dabarun samar da mafita ta tattalin arziki.

A cewar wasiƙar, maimakon yaƙar tsarin mulki daga sama, shrin  SAC na gina ɗaukar alhaki daga tushen al’umma, inda suka ƙaddamar da wani gwaji na farko (Proof of Concept – PoC) a wata unguwa da aka zaɓa a Kano ko Kaduna, wadda ke fuskantar matsin lamba mai yawa.

IG Wala  ya  ce za su mayar da ofishin Mai Unguwa ya zama cibiyar dijitai mai zaman kanta ta hanyar amfani da rajistar da ke aiki ko da babu intanet, domin tattara bayanai, bibiya, da tallafa wa yara masu rauni da ke rayuwar titi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *