Shugaban gwamnatin mulkin sojan Jamhuriyar Nijar, Abdourahamane Tiani, ya naɗa Janar Sani Issa Kashe a matsayin sabon jakadan ƙasar a Najeriya.
Nadin ya zo ne a wani mataki na sake fasalin wakilcin diflomasiyyar Nijar a wasu ƙasashe da cibiyoyin ƙasa da ƙasa.
- Girgizar asa mai ƙarfi ta kashe mutum 32 tare da jikkata ɗaruruwa a Venezuela
- Gwamnatin Tarayya ta gano tarin ma’adanai masu daraja a Jihar Kaduna
- Nijar ta miƙa buƙatar ficewa daga kotun ICC a hukumance
Haka kuma, gwamnatin Nijar ta sanar da tsige jakadan ƙasar a Ethiopia kuma wakilin Nijar a kungiyar tarayyar Afrika, Amadou Hassan Mai Dawa, daga mukaminsa.
Har yanzu hukumomin Nijar ba su bayyana dalilan da suka haifar da tsige jakadan ba.
Matakin na zuwa ne a yayin da gwamnatin mulkin sojan Nijar ke ci gaba da sake tsara harkokin diflomasiyya da hulɗar ƙasar da ƙasashen waje da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa.