Kwamishinan ’Yan Sanda na Babban Birnin Tarayya (FCT), Ahmed Mohammed Sanusi, ya umarci jami’an ’yan sanda masu kula da ofisoshin shiyya (DPOs) a yankin birnin Abuja da su kawo ƙarshen ayyukan fashi da makami da sauran laifukan sata a tsakiyar birnin cikin makonni biyu.
Sanusi ya bayar da wannan umarni ne a wani taro da ya yi da DPOs 17 da ke ƙarƙashin yankin Metro na Abuja a ƙarshen mako.
Kwamishinan ya bayyana cewa an shirya taron ne domin tantance halin tsaro da kuma inganta dabarun da za su taimaka wajen magance sabbin barazanar tsaro a Abuja.
Ya nuna damuwa kan matsaloli kamar fashi da makami a kan tituna da Satar motoci da laifukan “one chance” (inda masu laifi ke ɗaukar fasinjoji a mota su yi musu fashi) da direbobin da ke tuki a kan hanyar da ba ta dace ba da kuma sauran matsalolin da ke barazana ga lafiyar jama’a.
- Majalisar Dattawa na shirin sake tattauna ƙudirin kafa ’yan sandan Jihohi a zaman gaggawa
- Me ya sa Keir Starmer ya yi murabus daga mukamin Firayim Ministan Birtaniya?
- Rundunar ’Yan sanda ta yi tir da kisan gilla da aka yi wa wata mata bisa zargin satar yaro
- Firaministan Birtaniya Starmer ya yi murabus
Sanusi ya kuma gargadi jami’an da cewa duk wanda ya gaza aiwatar da umarnin zai fuskanci hukuncin ladabtarwa.
Har ila yau, ya nuna damuwa kan ayyukan masu baburan haya (okada) a manyan tituna da lalata kadarorin gwamnati da na jama’a da yin parking ba bisa ƙa’ida ba a kan manyan hanyoyi. da kuma cunkoson ababen hawa a cikin birnin.
Kwamishinan ‘yansandan na Abuja ya umarci DPOs da Kwamandojin Yankuna (Area Commanders) da su mayar da hankali sosai wajen tabbatar da tsaro a tsakiyar birnin Abuja, yayin da shi da kansa zai sa ido kan harkokin tsaro a yankunan bayan gari.
Haka kuma, ya umarci Kwamandan Metro da ya tabbatar da cikakken bin wannan umarni tare da kulawa sosai kan yadda ake aiwatar da shi, yana mai jaddada cewa ba za a lamunci sakaci ba.
Sanusi ya kuma roƙi mazauna Abuja da su ci gaba da bai wa ’yan sanda sahihan bayanai a kan lokaci domin taimakawa wajen yaƙi da aikata laifuka da inganta tsaro a babban birnin ƙasa.
Wannan umarni na zuwa ne a lokacin da hukumomi ke ƙara ɗaukar matakai domin rage ayyukan laifuka da tabbatar da tsaro ga mazauna Abuja.