Mariya Mahmood

Ministar Babban Birnin Tarayya Abuja (FCT), Dakta Mariya Mahmoud, ta nesanta kanta daga rahotannin da ke cewa an naɗa masu ba ta shawara guda bakwai.

An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da Mataimakiyarta ta Musamman kan Harkokin Yaɗa Labarai, Austine Elemue, ta fitar a ranar Litinin, inda ta bayyana rahotannin da ke danganta waɗannan naɗe-naɗe da ministar a matsayin masu yaudara da ruɗani.

A cewar Elemue, shi kaɗai ne jami’in yaɗa labarai da aka ba izinin fitar da sanarwar hukuma a madadin ministar.

Ofishin Ministar ya jaddada cewa duk wata sanarwa da Rano ya fitar bai kamata a ɗauke ta a matsayin daga Hukumar Gudanarwar Babban Birnin Tarayya (FCTA) ko kuma daga ministar ba.

Sanarwar ta kuma sake jaddada ƙudirin Dakta Mariya Mahmoud na tabbatar da gaskiya, riƙon amana da ingantacciyar sadarwa wajen gudanar da ayyukanta a matsayin Ministar Ƙaramar Hukumar Babban Birnin Tarayya (FCT).

Rahotanni sun nuna cewa Rano ya sanar da naɗin mataimaka guda bakwai a ƙarshen mako, inda ya ba su alhakin kula da fannoni daban-daban da suka haɗa da yaɗa labarai, ladabi da harkokin baƙi, harkokin ɗalibai, matasa da wasanni, harkokin addini da kuma ayyuka na musamman.

Idan dai za’a iya tunawa a karshen makon da ya gabatane wani mai suna Bin Usman Rano  wanda ɗan Ƙungiyar magoya bayan Dakta Mariya ne (Dr Mariya Support Group),  ya sanar da naɗin mataimaka bakwai, ciki har da masu ba da shawara kan harkokin yaɗa labarai, ladabi da tsari (protocol), al’amuran ɗalibai, matasa da wasanni, harkokin addini, da kuma ayyuka na musamman.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *