Gwamnatin Tarayya ta bai wa sababbin jakadu da manyan kwamishinoni huɗu Takardun Shaidar Diflomasiyya, wanda ke ba su damar fara aiki a hukumance a ƙasashen da aka tura su.                                                              

Jakadun za su wakilci Najeriya a ƙasashen Trinidad da Tobago, Kenya, Equatorial Guinea da Masar,

Miƙa takardun shaidar na daga cikin muhimman matakan diflomasiyya da ake kammalawa kafin jami’an su fara aikinsu a ƙasashen da aka naɗa su da wannan mataki jakadun sun samu cikakken ikon wakiltar Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, da kuma Tarayyar Najeriya a ƙasashen da za su yi aiki.

Ana sa ran sababbin jami’an za su taimaka wajen ƙarfafa alaƙar Najeriya da ƙasashen da aka tura su, musamman a fannonin kasuwanci, zuba jari, tsaro, ilimi, musayar al’adu da haɗin gwiwar yankuna.

Matakin ya zo ne yayin da Najeriya ke ƙara ƙaimi wajen amfani da diflomasiyyar tattalin arziki domin jawo ƙarin masu zuba jari daga ƙasashen waje tare da bunƙasa haɗin gwiwar ci gaba a Afirka da yankin Caribbean.

Haka kuma, jakadun za su kasance masu kare muradun Najeriya da kula da walwalar ‘yan ƙasar da ke zaune a ƙasashen da aka tura su.

Ana sa ran za su isa ƙasashen da aka naɗa su nan ba da jimawa ba, domin gabatar da takardun shaidarsu ga shugabannin ƙasashen kafin fara aiki a hukumance.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *